Jose Mourinho ya kafa bakin tarihin zama Kocin da kungiyoyi 3 su ka tsige a kasar Ingila

Jose Mourinho ya kafa bakin tarihin zama Kocin da kungiyoyi 3 su ka tsige a kasar Ingila

- Tottenham ta fattattki Jose Mourinho da ta nada Kocinta a karshen 2019

- Kungiyoyin Chelsea da Manchester United sun taba korar babban Kocin

- Shugaban Tottenham, Daniel Levy zai nemowa kungiyarsa mai horaswa

A ranar Litinin, 19 ga watan Afrilu, 2021, kungiyar Tottenham ta bada sanarwar cewa ta raba jiha da babban kocinta Jose Mourinho.

Sanarwar da ta fito daga shafukan kungiyar kwallon kafan ta tabbatar cewa Mourinho da sauran masu taimaka masa sun bar kulob din.

Bayan Jose Mourinho, Tottenham ta sallami masu horas da ‘yan wasanta, Joao Sacramento, Nuno Santos, Carlos Lalin da Giovanni Cerra.

KU KARANTA: Tottenham ta tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin Koci

Ba wannan ne karon farko da aka sallami Mourinho daga aiki a Ingila ba. Kafin yanzu kungiyoyin Chelsea da Manchester Utd sun taba korarsa.

Mourinho wanda ya canji Mauricio Pochettino ya shafe shekara daya da rabi a Tottenham, ya na mai harin cin kofin Carabao a karshen makon nan.

Har an fara lissafin kocin da ake gani zai maye gurbin Mourinho a Tottenham. Jaridar Express ta kawo masu horaswa 4 da ake hange a Landan:

1. Julian Nagelsmann

Akwai yiwuwar Daniel Levy ya na zawarcin kocin kungiyar RB Leipzig, Julian Nagelsmann ganin irin kokarin da yake yi a Jamus tun da ya canji Ralf Rangnick a 2019.

KU KARANTA: An kai wa motar tawagar ‘Yan wasan Real Madrid hari a Liverpool

Jose Mourinho ya kafa bakin tarihin zama Kocin da kungiyoyi 3 su ka tsige a kasar Ingila
Jose Mourinho ya bar Tottenham

2. Brendan Rodgers

Brendan Rodgers wanda ya maida Leicester City abin tsoro tun bayan da ya dawo Ingila bayan ya nuna kwarewarsa a kungiyar Celtic ya na cikin wadanda ake tunani.

3. Scott Parker

Wani koci da Tottenham za ta iya dauko wa shi ne Scott Parker mai horas da kungiyar Fulham. Ana ganin tsohon ‘dan wasan Ingilan zai gane matsalar Tottenham.

4. Max Allegri

Akwai yiwuwar tsohon kocin Juventus da AC Milan, Massimiliano Allegri ya zama sabon kocin Tottenham. An dade ana sa ran ganin Allegri mai shekara 53 a Ingila.

Tun a bara aka ji kishin-kishin din cewa Mai horas da kungiyar Tottenham, Jose Mourinho, ya fara samun matsala da wasu manyan ‘Yan wasansa a kulob dinsa.

Rahotannin sun ce kasa da watanni uku da karbar ragamar kungiyar, Mourinho ya samu kansa a tsaka mai wuya da taurarin Tottenham saboda tsarin horaswarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng