An kai wa motar tawagar ‘Yan wasan kungiyar Real Madrid hari a kasar Ingila

An kai wa motar tawagar ‘Yan wasan kungiyar Real Madrid hari a kasar Ingila

- Ana zargin magoya bayan Liverpool da rotsa motar kungiyar Real Madrid

- An fasa gilashin wata motar ‘Yan wasan da aka ajiye a filin wasan Anfield

- Jami’an tsaro za su yi bincike domin gano wadanda su ka yi wannan barna

‘Yan sandan shiyyar Merseyside sun fara gudanar da bincike a kan harin da aka kai wa ‘yan wasan kwallon kafan kungiyar Real Madrid a wajen filin Anfield.

A daidai lokacin da ake shirin wasan Real Madrid da Liverpool na gasar cin kofin nahiyar Turai, aka samu wasu bata-gari da su ka auka wa tawagar ‘yan wasan.

Rahotanni daga Sky Sports sun tabbatar da cewa an kai wa wata daga cikin motar tawagar bakin ‘yan kwallon hari inda aka yi nasarar rotsa tagar wannan mota.

KU KARANTA: ‘Yan fashi sun shiga gidajen ‘Yan wasan PSG, sun sace miliyoyi

An ga ma’aikatan kungiyar kwallon kafa na Liverpool na kasar Ingila su na dauke gilashin da ya tarwatse daga motar bayan aukuwar lamarin a ranar Larabar nan.

‘Yan jarida sun bayyana cewa an ga jami’an ‘yan sanda a gaban motar a lokacin da ake tattara ragowar gilashin motar abokan karawar na kungiyar Liverpool.

Tuni dai kungiyar Liverpool da jami’an tsaron Merseyside su ka fito su ka yi tir da wannan hari.

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa sun fara binciken abin da ya faru, su ka bada tabbacin cewa ba za a kyale duk wanda aka samu da hannu a wannan aika-aika ba.

KU KARANTA: Jerin 'Yan wasan kwallon kafan Najeriya da su ka fi kudi

An kai wa motar tawagar ‘Yan wasan kungiyar Real Madrid hari a kasar Ingila
Motar Real Madrid Hoto: www.marca.com/en
Asali: UGC

Jami’an ‘yan sandan ta bakin Cif Sufiritanda Zoe Thornton, sun ce an rika jefa wa motar kungiyar Real Madrid ‘wasu abubuwa’ da bai iya bayyana su ba a jawabinsa.

Jawabin jami’in tsaron ya ce an yi dace ba a iya tarwatsa cikin gilashin ba don haka babu abin da ya iya kai ga cikin motar, a dalilin haka babu wanda ya samu rauni.

Bayan jifa da aka yi, an kuma jirkita wurin da aka ajiye motocin ta yadda ba za a iya gani da kyau ba.

A jiya ne aka ji cewa mai rike da kambun Super Eagles, Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa kungiyar kwallon kafan Kano Pillars wanda ya bari a shekarar 2009.

Tsohon dan wasan na CSKA Moscow, Leicester City da Al Nasr ya ce ya tattauna da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a kan batun komawa tsohon kungiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel