Koci Jose Mourinho ya fara rigima da wasu ‘Yan kwallon Tottenham

Koci Jose Mourinho ya fara rigima da wasu ‘Yan kwallon Tottenham

Ana kishin-kishin din cewa Mai horas da kungiyar Tottenham, Jose Mourinho, ya fara samun matsala da wasu ‘Yan wasansa a kulob dinsa.

Rahotanni sun ce kasa da watanni uku da karbar ragamar kungiyar, Mourinho ya samu kansa a cikin tsaka mai wuya da manyan ‘yan wasa.

Zaman dadin Jose Mourinho a Tottenham ya fara zuwa karshe a sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta ke fama da shi a ‘yan makonnin nan.

Tottenham ta samu nasara a wasanni uku ne kacal cikin wasanni takwas da ta buga. Mourinho ya karbi kungiyar ne bayan korar M. Pochettino.

Mourinho ya fara samun matsala ne bayan tsohon ‘dan wasansa, Marcus Rashford ya taimakawa Manchester United wajen doke Tottenham.

KU KARANTA: Attajirin Afrika Dangote ya na da niyyar sayen Arsenal har gobe

Daga baya Tottenham ta shiga tsaka-mai wuya a hannun Chelsea a gida kafin Liverpool su doke su. Wannan dai ya fusata manyan kulob din.

Ana tunanin cewa Koci Jose Mourinho zai shiga matsala a Landan muddin kungiyar Norwich ta doke shi a wasan da za a buga a Yau Laraba.

Kocin ya samu sabani da Danny Rose wanda ya ke yunkurin barin kungiyar. Ba wannan bane karon farko da ya samu matsala da Ma’aikatansa.

Haka zalika an ce yadda sabon Kocin ya ke amfani da Tanguy Ndombele wanda kungiyar ta saya da tsada ya na batawa wasu Taurarin kulob din rai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel