Tottenham ta tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin Koci

Tottenham ta tabbatar da nadin Jose Mourinho a matsayin Koci

Jose Mourinho ya zama babban kocin kungiyar Tottenham a Ranar Larabam 20 ga Watan Satumban 2019. Hakan na zuwa ne bayan kungiyar ta fatattaki Mauricio Pochettino daga aiki.

A Ranar Talatar nan ne Tottenham ta kori Mauricio Pochettino. Jose Mourinho ya kasance bai da aikin yi tun cikin Disamban 2018 a lokacin da kungiyar Manchester United ta tsige sa daga aiki.

Shugaban kungiyar Tottenham, Daniel Levy, yayin da ya ke bayyana nadin Jose Mourinho a shafin kulob din, ya kira Kocin a matsayin gwarzon mai horaswa, wanda zai kawo cigaba.

Levy ya ce: “A Jose Mourinho mun samu daya daga cikin gawurtattun masu horas da ‘yan wasa a kwallon kafa. Ya san aiki, kuma zai kai kulob din ga nasara, kuma gwarzon mai horaswa ne.”

Tsohon kocin nan kungiyar Chelsea, da Manchester United ya sa hannu ne a kan kwantiragin da za ta kai zuwa karshen kakar shekarar 2022 zuwa 2023 kamar yadda kungiyar ta bayyana dazu.

KU KARANTA: Wenger ya samu wani muhimmin aiki mai tsoka a Hukumar FIFA

Fitaccen Kocin ya ke cewa: “Ina farin cikin aiki da wannan kulob mai tarihi da magoya baya masu kishi. Kyawun manyan ‘yan wasa da kuma masu tasowa a kungiyar ya sa na karbi aikin."

Jose zai fara wasansa na farko ne da zuwa gidan West Ham a nan birnin Landan inda zai nemi nasara tare da sababbin ‘yan wasansa. Karonsa na farko a Firimiya cikin watanni fiye da goma.

Shafin kulob din ya bayyana Kocin a matsayin wadanda su ka fi zarra a Duniya bayan ya lashe kofi 25. Mourinho ya nuna bajintarsa a FC Porto, Inter Milan, Chelsea, Real Madrid da Man Utd.

Kungiyar ta ke cewa: “Mourinho ya jada tarihi a gasar gida a kasashe hudu (Portugal, Ingila, Italiya, da Sifen) kuma ya na cikin Koci uku da su ka lashe gasar Turai da kungiyoyi biyu.”

Bayan nasara a gasar cin kofin Turai a Italiya da Portugal, Kocin ya lashe Gasar Firimiya na Ingila da Chelsea sau uku a shekarun 2005, 06 da 2015. Jose Mourinho ya na da shekaru 56 a Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel