Buhari bai kasa Cika alƙawurransa ba, Yana hakuri ne da wautar wasu mutane, Inji Gwamna Masari
- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari yace shugaba Buhari na da matuƙar hakuri yadda yake jure wautar wasu mutane
- Gwamnan yace Buhari bai bamu kunya ba, kuma bai gaza cika alƙawurran da ya ɗauka ya yin yaƙin neman zaɓensa ba
- Buhari dai ɗan asalin jihar Katsina ne, jihar da gwamna Masari yake mulki, ana ganin kodan ɗan jiharsa ne shiyasa yake kareshi haka
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana hakuri da wautar wasu mutane.
KARANTA ANAN: Ka fito ka faɗa mana gaskiyar rashin lafiyar dake damunka, Bishop Wale Ga Buhari
A wata fira da yayi da gidan Talabishin ɗin TVC, Masari yace a yayin da wasu shuwagabannin basa iya tsayuwa da matsanancin zargi, amma shi Buhari ya kasance mai hakuri.
Gwamna Masari ya kuma ce shugaban ƙasa bai gaza cika alƙawurran da yayi lokacin yaƙin neman zabe ba. Yana mai bayyana jam'iyya mai mulki da tsayayya da ta cancanci a dogara da ita.
Gwamnan yace duk wanda kaji yana cewa darajar jam'iyyar APC a wajen mutane ya faɗi, to yasani ana gane hakane kawai a lokacin zaɓe.
Ya ce misali mafi sauki shine abunda muka gani daga sabunta rijistar jam'iyya da kuma rijistar sabbin mambobi, daga nan zaku gane ba gaskiya bane abunda ake faɗa kan APC.
KARANTA ANAN: PDP ta hurowa Shugaba Buhari Wuta, Ta nemi ya sallami Sheikh Pantami
Masari ya ce: "Ina tunani har yanzun APC tafi kowacce jam'iyya ƙarfi, ita tafi kowacce tabbas kuma ta cancanci a dogara da ita. Kuma bana tunanin Buhari ya bamu kunya, a'a yana hakuri ne da mu"
"Kuma kar ku manta, munyi wani shugaban ƙasa duk da cewa shugaban farar hula ne amma baya ɗaukar wautar mutane. Amma shi Buhari ba haka yake ba, yana hakuri da komai."
Shugaba Buhari ya fito ne daga jihar Ƙatsina, jihar da gwamna Aminu Bello Masari yake mulki.
A wani labarin kuma PDP ta hurowa Shugaba Buhari Wuta, Ta nemi ya sallami Sheikh Pantami
Babbar jam'iyyar adawa PDP ta hurawa shugaba Buhari wuta kan ya sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami.
Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Uche Secondus, shi ne ya yi kira ga shugaban da ya sallami ministan matuƙar bai aje muƙaminsa da kansa ba.
Asali: Legit.ng