Buga kudi: PDP ta hurowa Shugaban kasa wuta, ta ce ya kamata a fatattaki Ministar kudi daga ofis

Buga kudi: PDP ta hurowa Shugaban kasa wuta, ta ce ya kamata a fatattaki Ministar kudi daga ofis

- PDP ta na so Shugaban kasa ya sallami Ministar kudi da tattalin arziki

- Jam’iyyar adawar ta zargi Zainab Ahmed da karya kan batun buga kudi

- Daga baya CBN ta fito ta gaskata kalaman da Gwamnan jihar Edo ya yi

Babbar jam’iyyar hamayyar Najeriya, PDP, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Ahmed.

Jaridar Punch ta ce jam’iyyar adawar ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ta hannun sakataren ta na yada labarai na kasa, Kola Ologbondiyan.

Kola Ologbondiyan ya soki matakin da gwamnatin tarayya na karyata rahoton buga Naira biliyan 60 da babban bankin kasa na CBN ya yi domin a toshe gibi.

KU KARANTA: Gaskiya ne, mun buga karin N60bn kwanaki - CBN

Jam’iyyar PDP ta yi tir da rawar da Ministar tattalin arzikin Najeriya, Zainab Ahmed, ta ke taka wa, ta zarge ta da kokarin yin rufa-rufa da yi wa jama'a karya.

Mai girma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya fara wannan bayani inda ya ce sai da gwamnatin tarayya ta sake buga Naira biliyan 60 a watan jiya.

Bayan gwamnan ya yi wannan magana, Ministar kudi ta fito ta karyata shi, ta ce sam gwamnatin tarayya ba ta buga karin kudi domin a kara wa jihohin kasar ba.

Daga baya gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya raba gardama, ya ce babban bankin kasar ya buga karin kudi domin a tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.

Buga kudi: PDP ta hurowa Shugaban kasa wuta, ta ce ya kamata a fatattaki Ministar kudi daga ofis
Ministar kudi na kasa, Zainab Ahmed
Asali: Twitter

KU KARANTA: Saba alkawarin da Jonathan ya yi ya sa mu ka hana shi zarcewa - Aliyu

A dalilin haka, PDP ta ce akwai bukatar a tsige Zainab Ahmed tun da gwamnan CBN ya fallasa yaudara, da boye-boye, da karyar gwamnatin nan ta APC mai-ci.

PDP ta ce tun da gwamnati za ta koma wa yawan cin bashi da buge-bugen kudi, ta tabbata cewa Muhammadu Buhari bai da dabarar da zai inganta tattalin arziki.

A cewar Ologbondiyan, maganar da gwamnan CBN ya yi, ta tabbatar da cewa gwamnatin APC ta rugurguza tattalin arziki, kamar yadda alkaluma su ke ta nuna wa.

Kwanaki aka ji Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fasa-kwai a kan kudin da aka raba wa jihohi a watan Maris, ya ce gwamnatin tarayya na cikin fatarar kudi.

Amma da ya ke jawabi, Godwin Obaseki ya ce mutane su daina ganin laifin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce tattalin arzikin kasar ne ya tabarbare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel