Babangida: Abin da ya sa Gwamnonin PDP su ka yi wa Jonathan zagon-kasa a zaben 2015

Babangida: Abin da ya sa Gwamnonin PDP su ka yi wa Jonathan zagon-kasa a zaben 2015

- Mu’azu Babangida Aliyu ya maida martani kan dakatar da shi da aka yi a PDP

- Tsohon Gwamnan Neja ya bayyana dalilinsu na juyawa Goodluck Jonathan baya

- Babangida Aliyu ya ce Dr. Jonathan ya saba alkawarin cewa zai yi wa’adi guda

Tsohon gwamna Mu’azu Babangida Aliyu ya tabbatar da cewa wasu gwamnonin jam’iyyar PDP sun juya wa Goodluck Jonathan baya a babban zaben 2015.

Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ya bayyana cewa wasu takwarorinsa sun yi kokari wajen ganin tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan bai zarce ba.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, tsohon gwamnan ya ce shi da wasu gwamnonin wancan lokaci sun yi wa Jonathan zagon-kasa ne saboda saba yarjejeniya.

KU KARANTA: Sanatan Borno ya zargi Gwamnoni da hura wutan rikici a jihohi

A cewar Babangida Aliyu, wanda ya yi mulki zuwa 2015, tsohon shugaban Najeriyar ya karya alkawarin da aka yi da shi na cewa ba zai nemi tazarce ba.

Aliyu wanda a lokacin shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ya ce sun gano cewa yankinsu zai tashi a tutar babu da ace an bar Goodluck Jonathan ya zarce.

Babban jigon na PDP ya ce gwamnonin Arewa sun mara wa Dr. Jonathan baya ya karasa wa’adin Marigayi Ummaru ‘Yaradua da nufin cewa zai yi wa’adi daya.

Ya ce: “Ana tsakiyar tafiya, sai Goodluck Jonathan ya hakikance a kan sai ya sake neman takara a 2015, wanda hakan ya saba wa yarjejeniyar da mu ka yi da shi.”

Babangida: Abin da ya sa Gwamnonin PDP su ka yi wa Jonathan zagon-kasa a zaben 2015
Muazu Babangida Aliyu

KU KARANTA: Tsohon shugaba Goodluck Jonathan zai yi takara a 2023

“A kan haka mu ka yi adawa da Jonathan. Amma kafin nan, Goodluck Jonathan ya samu goyon-baya daga gwamnonin Arewa da daukacin mutanen yankin.”

Aliyu ya ce ba daidai ba ne ace ya yi zagon-kasa, ya ce ya yi aiki ne a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Arewa da ya yi kokarin kare al’ummarsa.

Babangida Aliyu ya yi wannan bayani ne a matsayin martani a kan dakatarwar da jam’iyyar PDP ta reshen karamar hukumar Chachanga a jihar Neja ta yi masa.

Idan za ku tuna, a karshen watan jiya ne babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta reshen jihar Neja ta dakatar da tsohon gwamnan a kan abin da ya faru a zaben na 2015.

Daga baya manyan PDP sun zauna a kan batun, su ka soke matakin da shugabanninta na karamar hukumar Chachanga su ka dauka saboda matsayin Aliyu a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel