Hukumomin tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan yarin Edo

Hukumomin tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan yarin Edo

- Jami' an tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan gyaran hali a ke Ubiaja a karamar hukumar Esan kudu maso gabashin jihar Edo

- Hukumar NSCDC ta ce ta tura jami'anta yankin cikin gaggawa bayan ta samu labarin yunkurin balle kurkukun

- Sai dai kuma a kokarin su na daidaita lamarin, wasu daga cikin jami’an hukumar gyara halin da kuma ma’aikatan NSCDC sun samu raunuka

An dakile wani yunkuri na fasa gidan yari da ke Ubiaja a karamar hukumar Esan kudu maso gabashin jihar Edo, TVC News ta ruwaito.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC), reshen jihar Edo da sauran jami’an tsaro ne suka dakile yunkurin tserewar a ranar Laraba,15 ga watan Afrilu a cewar kakakinta, Richard Ogbebor.

KU KARANTA KUMA: Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan

Hukumomin tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan yarin Edo
Hukumomin tsaro sun dakile yunƙurin fasa gidan yarin Edo Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Ya ce: “Kwamandan NSCDC na jihar Edo ya samu kiran waya kuma mun hanzarta tattara jami’ai zuwa wurin.

“Lokacin da muka isa cibiyar gyaran halin, sai aka gano cewa fursunonin sun balle daga dakunansu na kurkuku kuma tuni suka shiga fada da jami’an gidan yarin.

“A kokarin su na daidaita lamarin, wasu daga cikin jami’an hukumar gyaran halin da kuma ma’aikatan NSCDC sun samu raunuka daban-daban.

"Tare da taimakon runduna ta 4 ta sojojin Najeriya, reshen rundunar yan sanda na Benin da kuma Edo, an sha karfin fursunonin kuma an mayar da su cikin dakunansu."

Ogbebor ya kuma bukaci mazauna Edo da su rika bai wa rundunar bayanai masu amfani game da masu aikata laifuka a tsakanin su.

KU KARANTA KUMA: Malaman addinin Kirista sun yi bude bakin Ramadana da yan uwa Musulmi

A wani labarin kuma, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa miyagun 'yan ta'adda kwayoyi a Najeriya.

An cafkesu ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da kuma Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a Abuja yayin da shi tare da kungiyarsa suka ziyarci ministan yada labarai da al'adu na kasar nan, Lai Mohammed.

Asali: Legit.ng

Online view pixel