An yi wa tsohon tauraron ƙungiyar Manchester fashi a gidansa

An yi wa tsohon tauraron ƙungiyar Manchester fashi a gidansa

- Barayi sun afka gidan dan kwallon kafa, Chris Smalling a birnin Rome a kasar Italy

- Sun kwace masa agogon mai tsada kirar Rolex da wasu kayayyaki masu muhimmanci

- Rundunar Yan sanda Italy na birnin Rome sun ce sun fara bincike kan lamarin

Wasu mutane dauke da bindigu a safiyar ranar Juma'a sun afka gidan dan kwallon kafa, Chris Smalling, sun yi masa fashi da iyalansa da yaransa a gidansa da ke kasar Italy, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahotanni, dan wasan yana cikin gidansa da matarsa da dansa mai shekaru uku a lokacin da mutanen sanye da takunkumin fuska suka kutsa gidan suka tilasta shi ya bude musu wurin da ya ke ajiye kaya masu muhimanci.

An yi wa tsohon tauraron ƙungiyar Manchester fashi a gidansa
An yi wa tsohon tauraron ƙungiyar Manchester fashi a gidansa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Sun tilastawa Smalling mika musu agogonsa na alfarma kirar Rolex da wasu kaya masu muhimmanci daga wurin ajiyar.

Matar Smalling, Sam, ta kira yan sanda misalin karfe 5 na asuba kuma daga bisani yan sandan sun isa gidan dan kwallon da ke mil 25 kudu da birnin Rome.

A halin yanzu yan sanda na cigaba da bincike a kan lamarin kuma Roma ta ce za ta tallafawa dan wasan.

KU KARANTA: Matawalle ya ɗauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta

Yana zaune ne tare da matarsa yar asalin birnin Manchester. Sun yi aure tun Yunin shekarar 2017 sannan suka haifi dansu na farko, Leo, daf da dawowarsu babban birnin na Italy.

Mai tsaron bayan ya kasance yana buga wa wasa a Rome tun bazarar 2019.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel