Yanzu-Yanzu: Ƴan Sakai sun bindige ƴan bindiga da dama a tsakiyar kasuwa a Zamfara

Yanzu-Yanzu: Ƴan Sakai sun bindige ƴan bindiga da dama a tsakiyar kasuwa a Zamfara

- 'Yan Sakai a garin Dansadau sun shiga kasuwa sun bindige wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne

- Sun aikata hakan ne a matsayin daukan fansar kashe wasu manoma uku da yan bindiga suka yi a Ruwan Tofa a ranar Alhamis

- Rahotanni daga garin sun nuna cewa an tura jami'an tsaro suna ta sintiri domin tabbatar da doka da oda

Wasu yan banga da aka fi sani da Yan Sakai, a ranar Juma'a, sun shiga kasuwar Dansadau a jihar Zamfara inda suka bindige wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne, Daily Trust ta ruwaito.

Yan sakan, mafi yawancinsu daga Ruwan Tofa da wasu garuruwa da ke makwabtaka da su sun shiga kasuwar inda suka kashe wadanda ake zargin a matsayin ramuwar gayya kan kashe manoma uku da aka yi a Ruwan Tofa a ranar Alhamis.

Yanzu-Yanzu: Ƴan Sakai sun bindige ƴan bindiga da dama a tsakiyar kasuwa a Zamfara
Yanzu-Yanzu: Ƴan Sakai sun bindige ƴan bindiga da dama a tsakiyar kasuwa a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Mazauna garin sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan kasuwa duk sun rufe shaguna sun tsere saboda tsoron abin da zai iya biyo baya na daukan fansar kashe yan bindigan.

DUBA WANNAN: Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

"Yansu haka ina cikin gida na, gawarwakin yan bindigan da aka kashe suna nan a kasuwa. A yanzu da na ke magana da kai, mutane suna zaman dar-dar ne game da abin da zai faru nan gaba."

Wani mazaunin garin, Alhaji Yau Dansadau ya shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa mutane na cikin tsoro a garin.

"Bayan ganin abin da ya faru, wasu da ake zargin yan bindiga ne sun gudu zuwa shaganuna, ofisoshin yan sanda da gidaje domin tsira ... jami'an tsaro na sintiri a garin a yanzu domin tabbatar da doka da oda," in ji shi.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Muhammadu Shehu kan batun yayin hada wannan rahoton amma ba a same shi ba a waya.

KU KARANTA: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Alhaji Abubakar Dauran shima bai amsa waya da sakon kar ta kwana da aka aike masa ba.

Wannan harin na zuwa ne awanni bayan Gwamna Bello Matawalle ya dakatar da wani basarake saboda bawa wani soja mai sayarwa yan bindiga makamai sarauta.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel