BBOG: Ƴan Nigeria sun ɗau addini a kai amma imaninsu sai a hankali, Aisha Yesufu

BBOG: Ƴan Nigeria sun ɗau addini a kai amma imaninsu sai a hankali, Aisha Yesufu

- Aisha Yesufu, daya daga cikin wadanda suka samar da fafutukar BBOG ta soki yadda wasu yan Nigeria ke ikirarin riko da addini amma babu imani da tausayi

- Yar gwagwarmayar ta yi wannan furucin ne a hirar da aka yi da ita a lokacin da ake jimamin shekaru bakwai da sace yan matan na Chibok ba tare da an ceto dukkansu ba

- Aisha Yesufu ta ce idan ta fita kasashen waje mutane kan nuna jimani da tausayi idan sun ga bajin BBOG a jikinta amma a Nigeria ba a damu da batun ba ko kuma a rika mata gatse

Aisha Yesufu, wacce tana cikin waɗanda suka samar da fafutukar ceton ƴan matan Chibok ta Bring Back Our Girls, BBOG, da yan Boko Haram suka sace ta ce yawancin yan Nigeria su kan ɗauki addini a kai amma imaninsu 'sai a hankali'.

Yar gwagwarmayar ta yi wannan furucin ne a yayin hirar da Legit.ng Hausa ta yi da ita a yayin da ake cika shekaru bakwai da sace yan matan sakandaren na garin Chibok.

BBOG: Ƴan Nigeria sun ɗau addini a kai amma imaninsu sai a hankali, Aisha Yesufu
BBOG: Ƴan Nigeria sun ɗau addini a kai amma imaninsu sai a hankali, Aisha Yesufu. Hoto: Vanguardngrnews/Aisha Yesufu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha

A jiya Laraba 14 ga watan Afrilu ne kakakin majalisar Amurka, Nancy Pelosi ta yi jimamin cika shekaru bakwai da garkuwa da yan matan na Chibok amma kawo yanzu takwarorinsu a Nigeria ba su ce uffan ba kan batun wanda hakan alama ce da za a iya cewa ba su damu da yaran ba.

A kan hakan, Yesufu ta ce, "Ai wannan ba sabon abu bane ba, mu yawancin yan Nigeria sai ka ganmu mun dau addini a kai amma imaninmu kuwa abin sai dai a hankali."

Ta cigaba da cewa shekaru kadan bayan sace yan matan Chibok duk inda za ta tafi a duniya ta kan saja baji na BBOG a jikinta don cigaba da janyo hankali game da batun kuma mutanen kasashen waje su kan nuna tausayi da addu'ar Allah ya fito da yaran.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak

Amma mafi yawancin yan Nigeria gatse suke mata idan sun ga bajin domin ba su tausayawa halin da yaran da iyayensu ke ciki suna maganganu kamar "Har yanzu kuna nan kuna saka wannan bajin? Au, har yanzu ba a dako su ba?" da sauransu.

Daga karshe Aisha Yesufu ta shawarci gwamnati zage damtse don ganin an ceto sauran yaran kuma ta rika ganawa da iyayen yaran tana yi musu bayanin abin da ke faruwa tare da kwantar musu da hankali.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel