Dakarun soji ne ke rike da Damasak, ba 'yan Boko Haram ba, Hukumar soji
- Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta musanta labarin dake cewa 'yan ta'adda sun kwace garin Damasak
- Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar, tabbas 'yan ta'adda sun kai hari amma sojoji ke rike da garin a halin yanzu
- Ya ce Birgediya Janar S.S Tilawan ya yawata garin da rana kuma ana cigaba da kokarin kakkabo ragowar 'yan ta'addan
Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce rundunarta ta Operation Lafiya Dole ce ke rike da garin Damasak dake karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.
A ranar Talata ne aka tabbatar da cewa 'yan ta'addan Boko Haran sun kai farmaki garin.
Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a garin Abuja.
Yerima ya ce rahotannin da wasu bangare na kafafen yada labarai ke bayyana na cewa 'yan ta'adda sunkwace garin Damasak duk babu gaskiya a ciki.
KU KARANTA: Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta
KU KARANTA: Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari
Ya ce tabbas 'yan ta'addan sun kai farmaki garin amma kuma cike da kwarewa zakakuran sojin suka fatattake su.
"A halin yanzu da muke magana, dakarun ne ke rike da yankin. Kwamandan birged ta biyar, Birgediya Janar S.S Tilawan na yawo a garin domin duba yadda garin yake bayan harin 'yan ta'adda," yace.
Daraktan yace 'yan ta'addan sun shiga garin ta yankin arewaci tare da hadin bakin wasu mazauna yankin.
"Rundunar sojin kasa na tabbatar wa da mazauna Damasak da yankunan kusa da su kwantar da hankalinsu domin ana cigaba da kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake wasu sassan garin," yace.
A wani labari na daban, wasu sojin Najeriya da ke fama da yaki da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas sun shirya wata waka ta sukar miyagun 'yan ta'addan.
A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga sojojin suna waka yayin da wasu ke amshi tare da yin bidiyo.
A wakar, an ji zakakuran sojin suna kira ga 'yan ta'addan da su daina fakewa da Allah suna barna tare da nuna cewa suna yin kisa saboda Allah ne. Allah mai girma ne da buwaya kuma baya kashe jama'a.
Asali: Legit.ng