Rundunar Yan Sanda Sun sheƙe wasu yan fashin teku 4 a jihar Akwa Ibom
- Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar hallaka wasu mutane huɗu da ake zargin yan fashin teku ne
- Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar d faruwar lamarin, inda ya ce yan sanda a Marine, ƙaramar hukumar Oron sun fita sintiri ne bayan samu ƙwararan bayanai.
- Ya ce an samu nasarar ƙwato jirgin ruwa mai matuƙar gudu, bindigu guda biyu da kuma harsasai shida daga hannun waɗanda ake zargin
Wasu mutane huɗu da ake zargin yan fashin teku ɓe sun gamu da ajalinsu a wata musayar wuta da suka yi da rundunar yan sandan Marine ƙaramar hukumar Oron, jihar Akws Ibom.
KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya
An kashe waɗanda ake zargin ne a wani sintiri da jami'an suka fita a Ikang Creek bayan samun bayanai akan yan fashin kamar yadda Punch ta ruwaito.
A wani jawabi da kakakin yan sandan jihar, Odiko Macdon, ya fitar ranar Laraba, wanda ya yi ma take da "Tsaftace hanyar ruwa a jihar Akwa Ibom" ya ce, sun kwato jirgin ruwa mai tsananin gudu da lamba 115HP, bindigu guda biyu, da kuma harsasai dag hannun mutanen.
A bayanin kakakin yan sandan, ya ce waɗanda ake zargin sun kai su 32, a cikin juragen ruwa 4 sun buɗe wuta ga jami'an yan sandan tunda suka yi ido huɗu da su.
A wannan batakashi da aka yi, huɗu daga cikin yan fashin sun rasa ransu, sauran kuma suka gudu a cikin jiragen ruwa uku.
KARANTA ANAN: Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa
A bayanin nasa ya ce:
"Ya yin ɗaukar mataki akan kwararan bayanan da suka samu ranar 13 ga watan Afrilu, jami'an yan sanda dake Marine ƙaramar hukumar Oron sun fita sintiri Ikang Creek, Oron, inda suka yi kiciɓus da yan fashin teku, su 32 ɗauke da manyan makamai."
"Waɗannan yan fashin suna ganin jami'an sai suka buɗe musu wuta. A ya yin wannan musayar wuta ne aka kashe huɗu daga cikin yan fashin tekun, sauran kuma suka tsere a cikin jiragen ruwa uku."
"An kuma kwato jirgin ruwa mai injin Yamaha, bindigu guda biyu, da kuma harsashi 6 daga hannun waɗanda ake zargin."
A wani labarin kuma Jiragen Yaƙi shida daga Amurka Zasu iso Najeriya a watan Yuli, 2021 - Inji Fadar shugaban ƙasa
Gwamnatin tarayya tace jirage shida daga cikin 12 da ta siya daga ƙasar Amurka zasu iso Najeriya a tsakiyar watan Yuli, don ƙara ma rundunar Sojin sama ƙarfin gwuiwa.
Babban mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Garba shehu, shine ya bayyana haka.
Asali: Legit.ng