Gwamnan Yobe an angwance da diyar marigaryi Abacha, Hajiya Gumsu
- Bayan mutuwar aurenta, diyar marigayi Janar Sani Abacha, Gumsu, ta sake aure
- Gumsu ta auri gwamnan jihar Yobe kuma shugaban rikon kwaryan jam'iyyar APC
- An yi taron daurin auren ne a gidan babban yayan Gumsu, Mohammad Abacha dake Abuja
Wani rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Laraba, 14 ga afrilu ya auri matarsa ta hudu, Gumsu Sani Abacha.
Sabuwar Amaryar diya ce ga tsohon shugaban kasan mulkin Soja, marigayi Janar Sani Abacha.
A cewar rahoton, Buni wanda shine shugaban rikon kwaryan jam'iyyar APC ya bada kwabon zinari 24 matsayin sadaki.
An gudanar da taron daurin auren ne a birnin taraya Abuja, gidan babban yayan amarya, Mohammed Abacha.
DUBA NAN: Yan bindiga kai farmaki kwalejin Soji dake Kaduna
KU KARANTA: Hotunan auren yar gwamnan Kebbi da tsohon kakakin majalisa, Hon. Dimeji Bankole
Gumsu, mai shekaru 45, a baya ta auri wani attajirin kasar Kamaru, Bayero Mohamadou, har tsawon shekaru 20 kafin suka rabu a 2020.
Daga cikin manyan da suka halarci taron akwai kwantrola janar na kwastam, Hameed Ali; kwamishanan yan gudun hijra, Bashir Garba-Lado, Sanata Lado DanMarke, dss.
Buni ya auri matarsa ta hudu bayan auren diyar magabacinsa, Adama Ibrahim-Gaidam, a shekarar 2019.
A bangare guda, tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole a ranar Juma'a 15 ga watan Janairu ya angwance da Aisha Shinkafi Saidu, diyar gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Bankole, wanda ya rabu da matar sa ta farko a shekarar 2017, ya kasance mai matukar neman haihuwa cikin rukunin wadanda suka cancanta a ciki da wajen Najeriya.
Bikin auren rufe labule kan jita-jita dangane da niyyar aurensa tun bayan sakin.
Asali: Legit.ng