Bayan ta kafa tarihin fita da sakamako mafi kyau a jami'a, yar Nageriya ta samu tallafin zuwa Amurka
- Wata kwararriyar yar Najeriya, Ofure Ebhomielen, ta baiwa mutane mamaki a lokacin karatun ta na digirin farko a jami'ar Ibadan (UI)
- Matar ta bayyana cewa babu wani ƙarshen zangon karatun jami'a da baza ta ci sakamako CGPA 7.0 ba, ta ce har a aji na uku wanda yafi bata wahala
- Amma yanzun zata zama ɗalibar Standford, ɗalibar ta ce karatu a ƙasashen waje yafi sauƙi sosai babu takura akan na Najeriya
Wata matashiya yar Najeriya, Ofure Ebhomielen, ta karya tarihin fita da sakamako a jami'ar Ibadan (UI) a matsayin ɗaliba mace ta farko da ta ci 7.0 a gaba ɗaya sakamakonta har ta gama jami'ar.
KARANTA ANAN: Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya
A wata zantawa da tayi da Legit TV, Ofure ta bayyana cewa ita ce ɗaliba ta huɗu data sami makamancin wannan sakamakon.
Bayan wannan babbar nasarar da ta samu Ofure ta sami tallafin cigaba da karatunta na digiri na biyu a jami'ar Standford, Amurka.
A lokacin karatunta a UI, Ofure ta ce yan uwanta ɗalibai sun santa ne sanda tazo aji na biyu, daga nan ta fara taimaka ma ɗalibai wajen karatunsu.
Ɗalibar mai basira ta iya tuna lokacin data fusakanci babban ƙalubale a ajinta na uku a darasin lissafi (Mathematics). Ta ce, wani abokin ta, Olawale Ahmed, shine ya koya mata darasin.
KARANTA ANAN: Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19
Da aka tambayeta ko ya taji da ta sami tallafin karatu zuwa Amurka, Ofure ta bada amsa cikin barkwanci inda ta ce:
"Na cike neman takardar izinin karatun (Admission), amma sai da na faɗa ma mai kula damu a jami'a cewa bazan iya ɗaukar nauyin wannan karatun ba sabida canjin dala zuwa naira ya tashi sosai."
Ofure ta ce tallafin karatun ya iso gareta ne a lokacin da take cin abinci. Ta ƙara da cewa karatu a Amurka yana da wahala sabida a cewarta zata ji kamar an tsuke ta ne idan ta ɗauki darasi biyu kacal a zangon karatu.
Ba kamar a Najeriya ba ind take iya ɗaukar darussa 14 a zangon karatu ɗaya.
Daga ƙarshe, Ofure ta bayyana matakan samun nasara da suka haɗa da aikin gida, gwaji akai-akai sune hanyoyin da ɗalibai ke sanin inda suka dosa a sakamakon su.
A wani labarin kuma A karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Alkalin jihar
Gwamnan jihar Nasarawa , Abdullahi Sule, ya rantsar da mace mai suna Aisha Bashir Aliyu a matsayin shugabar alƙalai (CJ).
Aisha dai ta zama ita ce mace ta farko a jihar da zata riƙe wannan babban muƙami, wanda hakan ya zama babban ƙalubale a gabanta musamman tazo dai-dai lokacin da ma'aikatan shari'a ke yajin aiki.
Asali: Legit.ng