Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

Fitacciyar Jaruma dake shirya Fina-Finai ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya

- Sananniyar jaruma kuma ma'aikaciyar gidan talabishin ta rigami gidan gaskiya bayan kwanciya a Asibiti na ɗan ƙanƙanin lokaci

- Ɗan uwan jarumar kuma ƙaninn ta ne ya tabbatar da rasuwarta a wata zantawa da aka yi dashi ta wayar salula

- Kafin jarumar ta rasu ta samu lambobin yabo da dama, kuma ta yi aiki da gidan talabishin na NTA a lokacin da ta yi aikin bautar ƙasa

Jarumar shirya fina-finai kuma ma'aikaciyar gidan tababishin, Rachel Bakam, ta rigamu gidan gaskiya kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Bakam, wacce ta fito daga Fadiya Tudun Wada a ƙaramar hukumar zangon kataf ta rasu ne tana da shekaru 39 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne ranar Talata da yamma bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa, Abuja.

Bakam Adams Junior, wanda ƙanine dake bin jarumar, shine ya tabbatar da rasuwar yayar tasa a wata tattaunawa da aka yi da shi ta wayar salula.

Ya bayyana cewa yayar tasa ta rasu ne a asibiti mai zaman kansa a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wata Sananniyar Jarumar Fim ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya
Wata Sananniyar Jarumar Fim ta rigamu gidan Gaskiya bayan fama da gajeruwar Rashin lafiya Hoto: #Rachelbakam
Asali: Facebook

KARANTA ANAN: Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku

Junior ya ce: "Labarin da kukaji na rasuwarta gaskiya ne, mun kwantar da ita a asibiti ranar Jumu'a, ta rasu ranar Talata da yamma bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya."

"Ta rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa a babban birnin tarayya Abuja."

Junior ya ƙara da cewa, rasuwar yar uwar tasa ya jawo babban naƙasu da iyalan gidan su.

Ya ce: "Rach kamar yadda muke kiranta mutum ce mai kaunar jama'a, bata da son kai, kuma tana da addini da tsoron Allah. Mutuwarta ta matuƙar girgiza mu, ni har yanzu ban dawo dai-dai ba, shiyasa ba zan iya bayyana muku komai ba."

Richael Bakam ta mutu ta bar ɗa guda ɗaya, da mahaifiyarta da yan uwa maza uku dadai sauran danginta.

A wani labarin kuma Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba

Ministan Sadarwar ƙasar nan, Isa Pantami,ya ƙara jaddada matsayarsa kan kulle duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da NIN ba.

Ministan ya faɗi haka ne a wani jerin saƙonni da ya fitar a shafin sa na Tuwita ya yin da yake martani kan wani labarin ƙanzon kurege da ake jingina mishi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel