Boko Haram sun kafa tuta, an fatattaki mutum 100, 000 daga garin Damasak zuwa kasar Nijar

Boko Haram sun kafa tuta, an fatattaki mutum 100, 000 daga garin Damasak zuwa kasar Nijar

- Boko Haram sun yi wa garin Damasak zobe har ta kai sun kafa tutarsu a makon nan

- ‘Yan ta’addan Boko Haram sun kona gidajen Sanata Abubakar Kyari da ‘Dan Majalisa

- Ana maganar mutane 100, 000 su ka sulale zuwa Nijar bayan wadannan hare-haren

Rahotanni daga Daily Trust sun tabbatar da cewa sama da mutane 100, 000 su ka fice daga garin Damasak, jihar Borno, su ka tsallaka Jamhuriyyar Nijar.

A ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021, ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram su ka sake kai hari wanda shi ne na shida a cikin kwana goma a garin Damasak.

Boko Haram sun addabi babban birnin na karamar hukumar Mobbar a ‘yan kwanakin nan, hakan ya yi sanadiyyar da mutane su ka yi gudun hijira zuwa Nijar.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari a Makarantar Sojoji a garin Kaduna

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘yan ta’addan sun shiga Damasak sun ci karensu babu babbaka, sun yi kone-kone, sannan sun hallaka Bayin Allah.

Kamar yadda mu ka samu labari, cikin wuraren da aka kona har da gidjen Sanata Abu Kyari da ‘dan majalisa mai wakiltar yankin Mobbar, da ofishin ‘yan sanda.

Har zuwa yanzu da ake tattara rahoton, garin Damasak ya na hannun Boko Haram, har ta kai ‘yan ta’addan sun kafa tuta kamar yadda su ke yi idan sun karbe gari.

Sojojin kasa da dakarun sojojin saman Najeriya su na cigaba da kokarin karbe wannan babban gari mai tarihi daga hannun wadannan ‘yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun hallaka wasu barayin kan teku a jihar Akwa Ibom

Boko Haram sun kafa tuta, an fatattaki mutum 100, 000 daga garin Damasak zuwa kasar Nijar
Gwamnan Borno garin Damasak kwanaki
Asali: Twitter

Tsakanin Damasak da ke Arewacin jihar Borno da garin Maiduguri, tafiyar kilomita 188 ne. wannan gari ya yi iyaka da Jamhuriyyar Nijar da yankin tafkin Chadi.

Wani Bawan Allah da ya koka wa Duniya ta waya, ya ce duk wadanda za su iya fice wa daga Damasak sun bar gari, kafin sojoji su rufe iyakokin Gamari da Kareto.

Kamar yadda wannan mutum ya bayyana, da-dama daga cikin wadanda su ka mutu, ba su samu jana’iza ba, ya ce kusan 50% na mutanen garin sun tsallaka zuwa ketare.

A jiya ne ku ka ji an tabbatar da mutuwar mutane goma a harin da Boko Haram su ka kai a daren ranar Talata a garin Damasak, bayan kone-konen da aka yi kwanan nan.

Shugaban karamar hukumar Mobbar, Mustapha Bako Kolo ya bayyana wannan da aka yi hira da shi. Har yanzu sojojin Najeriya ba su fito sun yi bayanin halin da ake ciki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel