Kokarin karfafa Majalisa da Kotu ta hada Shugaba Buhari yaki da Gwamnonin Jihohi 36

Kokarin karfafa Majalisa da Kotu ta hada Shugaba Buhari yaki da Gwamnonin Jihohi 36

- Gwamnatin Tarayya ta na yunkurin ba 'Yan Majalisa da Kotun jihohi ‘yancin gashin-kai

- Amma da alamu Gwamnonin ba su so Kotu da Majalisun dokoki su zauna da kafafunsu

- Gwamnan Filato, Simon Lalong ya soki dokar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo

A ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021, gwamnoni su ka nuna rashin goyon bayan dokar da shugaban kasa ya kawo na ba majalisa da kotu ‘yancin-kai.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa gwamnonin jihohi ba su kan shafi guda da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan lamarin.

Kungiyar gwamnoni na kasa watau NGF ta fitar da jawabi ta na cewa ita ba ta adawa ga yunkurin ba majalisar dokoki da kotun jihohi damar cin gashin kansu.

KU KARANTA: Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Gwamna Matawalle

Amma kungiyar NGF ta ce ba za ayi mata karfa-karfa da wannan doka da shugaban kasa ya kawo ba.

A cewar gwamnonin, ba a bukatar dokar da shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba wa hannu wajen ba majalisa da bangaren shari’a ‘yancin-kai ta fuskar kudi.

Gwamnonin jihohin ta bakin Simon Bako Lalong sun bayyana cewa shugaban kasa bai tuntube su kafin ya kawo wannan doka mai cikakken iko mai lamba ta goma.

Gwamna Simon Bako Lalong ya fitar da jawabi ne a Abuja a madadin sauran abokan aikinsa bayan NGF ta yi zama da Ministan kasuwancin Faransa, Franck Riester.

Kokarin karfafa Majalisa da Kotu ta hada Shugaba Buhari yaki da Gwamnonin Jihohi 36
Gwamna Simon Lalong
Asali: UGC

KU KARANTA: Yadda ‘Buhari’ ya sa na shiga APC - Gwamnan Ebonyi

A lokacin da gwamnoni ke adawa da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka, AGF, Abubakar Malami, ya bayyana cewa ba za a janye wannan doka da aka shigar ba.

Simon Bako Lalong ya ce tun farko babu dalilin kawo wannan dokar, ya ce dokar ce ta haddasa rashin fahimtar da ta sa ma’aikatan shari’a su ka tafi yajin-aiki a Najeriya.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa za a zauna domin ganin yadda za a bi wajen dabbaka dokar.

A jiya ku ka ji cewa duk da Shugaban kasa ba ya Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da manyan nade-naden mukamai da aka yi a ma'aikatun NBTE, NCCE da NSSEC.

Ministan ilmi ya nada shugabannin da za su kula da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya. Farfesoshi biya su ka samu kujeru a Gwamnatin Buhari a mukaman da aka bada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel