Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle (Hotuna)

Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle (Hotuna)

Gwamnoni tara da tsaffin gwamnoni da dama suna daga cikin wadanda suka hallarci daurin auren 'yar gwamnan jihar Zamfara, Ruqayya Matawalle a ranar Asabar a garin Maradun.

Gwamonin sun hada da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal; gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya; gwamnan Imo, Chukwuemeka Ihedioha; gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow da gwamnan Borno, Babagana Zulum.

Tsaffin gwamnonin da suka hallarci daurin auren sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso, Sule Lamido da Ahmad Sani.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Gwamna Tambuwal shine waliyin amaryar Ruqayya inda ya bayar da ita ga wakilin angon, Madakin Katagum, Alhaji Abdullahi Babani a auren da aka dayura a fadar sarkin Maradun.

Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle
Gwamna Matawalle tare da amarya Ruqayya da angon ta
Asali: Twitter

Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle
Gwamna Aminu Tambuwal da Mai martaba Sarkin Maradun tare da Gwamna Bello Matawalle a wurin daurin aure
Asali: Twitter

Gwamnoni 9 sun hallarci daurin auren 'yar Matawalle
Ruqayya Matawalle da angonta
Asali: Twitter

An daura auren kan sadaki naira N100,000 da aka biya lakadan.

Gideon Sammani, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wurin daurin auren.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa 'yan majalisar tarayya da na jihar da manyan 'yan siyasa da sarakuna da masu rike sa sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na kasar sun hallarci daurin auren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel