Duk da Shugaban kasa ba ya nan, Gwamnatin Tarayya ta fitar da manyan nade-naden mukamai

Duk da Shugaban kasa ba ya nan, Gwamnatin Tarayya ta fitar da manyan nade-naden mukamai

- Shugaban kasa ya amince da nadin sababbin shugabannin ma’aikatun Gwamnati

- Ma’aikatar ilmi ta ce an nada sakatarori a ma’aikatun NBTE, NSSEC, da ta NCCE

- Farfesa Idris Bugaje, Abdullahi Abba, da kuma John Enaohwo sun samu kujeru

A ranar Laraba, 14 ga watan Afrilu, 2021 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu nadin mukamai a ma’aikatar ilmi ta tarayya.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa shugaban Najeriyar ya yi nadin mukaman ne a ma’aikatun NBTE, NSSEC, NCCE da kungiyar UNESCO.

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ilmi ta ce shugaban kasa ya nada Farfesa Idris Muhammad Bugaje a matsayin babban sakataren ma’aikatar NBTE.

KU KARANTA: Minista ya lauye bayan an tambaye shi a kan dawowar Buhari

Idris Muhammad Bugaje wanda ke shugabantar makarantar Kaduna Polytechnic ya zama shugaban ma’aikatar da ke kula da makarantun fasaha.

Kamar yadda mai magana da yawun bakin ma’aikatar ilmin tarayya, Ben Goong, ya bayyana, Dr. Benjamin Abakpa ya zama shugaban ma’aikatar NSSEC.

Har ila yau gwamnatin tarayya ta nada Farfesa Paulinus Okwelle a matsayin babban sakataren hukumar NCCE mai kula da makarantun horas da malamai.

Shi kuma Farfesa John Enaohwo shi ne wanda zai lura da majalisar da ke kula da aikin NCCE.

Duk da Shugaban kasa ba ya nan, Gwamnatin Tarayya ta fitar da manyan nade-naden mukamai
Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanusi ya ce bashin da ke kan Gwamnatin Tarayya ya karu da 400%

Sanarwar ta ce Farfesa Abdullahi Abba ya zama sabon shugaban majalissar da ke kula da babbar jami’ar kiwon lafiya ta tarayya da ke garin Otukpo, Benuwai.

Ben Goong a madadin Ministan ilmi na tarayyar Najeriya, ya ce wadanda aka ba wadannan mukami za su fara aiki a ranar Juma’a 16 ga watan Maris, 2021.

Shi kuma Farfesa Ibrahim Muhammad ya zama Darekta a cibiyar harshen larabci da ke Ngala, yayin da Hajo Sani ta zama wakiliyar Najeriya a kungiyar UNESCO.

Dazu kun samu cikakken rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada hadimar Mai dakinsa, Dr. Hajo Sani matsayin jakadiyar Najeriya a UNESCO.

Wannan nadin na zuwa ne kasa da sati daya bayan an kaddamar da littafin da ta rubuta a kan rayuwar mai dakin shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel