Bincike: Shin da gaske kasar China ta kwace jirgi cike da mazakutan mutum 7200 daga Najeriya?

Bincike: Shin da gaske kasar China ta kwace jirgi cike da mazakutan mutum 7200 daga Najeriya?

Femi Fani-Kayode, wani tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya yi ikirari a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa “an kama wani jirgi daga Najeriya a China yayin da yake kokarin yin fasakwaurin mazakuta 7,200.”

Jigon na PDP ya kuma yi ikirarin cewa "dubunnan dubatan mazakutan 'yan Najeriya ake shigo da su (sin) China a kowace shekara."

A karshe, ya yi ikirarin cewa "Najeriya ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da mazakuta", ya kara da cewa "wannan shine dalilin da ya sa sace-sace da kashe-kashe na tsafi ya zama ruwan dare a nan."

Gaskiyar zance

Ikirarin yawancinsa karya ne. Binciken Legit.ng ya nuna cewa ikirarin ya dogara ne da wani labari wanda ya samo asali daga wani shafin yanar gizo mai cike da rubutun zolaya wanda aka yiwa lakabi da World News Daily Report (WNDR)

DUBA NAN: Hotunan kamfen din takarar shugaban kasa na Bukola Saraki sun cika garin Abuja

Bincike: Shin da gaske kasar China ta kwace jirgi cike da mazakuta daga Najeriya
Bincike: Shin da gaske kasar China ta kwace jirgi cike da mazakuta daga Najeriya Hoto: africadailynews.net
Asali: UGC

Cikakken Bayani

A ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode, ya yi ikirarin a zaren sakonnin Tuwita cewa jirgin da ke dauke da mazakuta 7,200 daga Najeriya ya shiga kasar China.

Ya kuma yi ikirarin cewa ana safarar dubunnan dubatar mazakutan 'yan Najeriya zuwa kasar China duk shekara.

Tsohon ministan ya kara da cewa Najeriya ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da su. A cewarsa, wannan ne ya sa satar mutane da kashe-kashen tsafi suka zama ruwan dare a Najeriya.

Ya rubuta cewa:

“An kama wani jirgi daga Najeriya a kasar China yayin da yake kokarin yin fasakwaurin mazakuta 7,200. Dubunnan dubatan mazakutan 'yan Najeriyar ake fasa kwaurinsu zuwa China a kowace shekara.
"Najeriya ce kan gaba a duniya wajen fitar da mazakuta kuma wannan shi ya sa satar mutane da kashe-kashe na tsafi suka zama ruwan dare a nan."

Ya zuwa yammacin ranar Laraba, 14 gawatan Afrilu, lokacin da Legit.ng ta hango rubutun a Tuwita, an watsa shi sama da sau 700 tare da kusan mutane 2,000 da suka yi masa dankwale.

Tantance gaskiya

Ikirari na 1: Kasar China ta kwace mazakuta 7,200 daga Najeriya

Tsohon ministan bai bayyana asalin inda ya dauko wannan ikirarin ba.

Sai dai, bincike mai mahimmanci da Legit.ng ta gudanar ya gano cewa ikirarin yana kunshe cikin labarin da wani shafin yanar gizo na "zolaya" ya buga mai suna World News Daily Report (WNDR).

Taken dandalin labarai, Legit.ng ya gano a shafinsa na yanar gizo, shine Rahoton Labaran Duniya na Yau da Kullum, Inda Gaskiya Ba Ta Da muhimmanci.

Har ila yau, a cikin sashinsu na "Game da Mu", World News Daily Report ta ce "tana daukar duk wani nauyi na dabi'ar zolaya da labaran nata da kuma yadda ake kirkirar labaransu."

Ya kara da cewa:

"Dukkanin haruffan da suka bayyana a cikin wannan shafin na yanar gizo - har ma wadanda suka danganci mutanen kwarai - duk kirkirarren labari ne kuma duk kamannin da ke tsakanin su da kowane mutum, mai rai, ko wanda ya mutu ba, mu'ujiza ce kawai."

A halin yanzu, wasu shafukan na binciko gaskiya kamar Boom Live da PolitiFact sun bayyana dandalin a matsayin "wani shahararren gidan yanar gizo na labarai ne na karya, wanda yake bayar da bayanan karya ta hanyar fakewa da bayanan sirri."

Ikirari na 2: Dubunnan dubatan mazakutan 'yan Najeriya ake shigo da su kasar China kowace shekara

Kamar na farko, Fani-Kayode bai bayyana tushen wannan ikirarin ba. Legit.ng ba ta iya samun wani tabbataccen wadataccen bayani da ke tallafawa ikirarin ministan ba.

Ikirari na 3: Najeriya ce kan gaba a duniya wajen fitar da mazakutan

Hakazalika, babu wani tabbataccen wadataccen bayani dake goyon bayan ikirarin tsohon ministan na cewa Najeriya ita ce kasar da ta fi kowace kasa fitar da mazakuta a lokacin hada wannan rahoton.

Domin kara tabbatarwa, Legit.ng ta aike da sako zuwa ga Fani-Kayode ta shafin Tuwita tana neman sa da ya ba da tushen maganganun. Har yanzu bai amsa sakon ba.

Kammalawa

Ikirarin da tsohon ministan ya yi galibi karya ne saboda sun nuna galibi an same su ne daga wata kafar yanar gizo da ya bayyana a karara cewa hujjoji ba su da wata ma'ana a garesu.

KU KARANTA: JAMB ta soke amfani da Email a dawainiyar rajistar jarrabawarta

A wani labarin, Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Zee-zee ta leko Instagram biyi bayan jita-jitan mutuwar ta, ta ce tana raye daram ba ta mutu ba.

A makon da ya gabata ne aka shiga rudu da mamaki biyo bayan samun labarin da ya fito daga shafin na Instagram cewa ta rasu.

Sai dai tsohuwar jarumar ta ce ta shiga dogon suma ne ba mutuwa ba, wanda hakan ya sa kawarta wadda a lokacin tana gidanta ne ta yi tsammanin ta rasu bayan ta yi ta zuba mata ruwa amma ba ta farfado ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel