Ban mutu ba, dogon suma na yi saboda tsananin rashin lafiya, in ji Ummi Zee-Zee

Ban mutu ba, dogon suma na yi saboda tsananin rashin lafiya, in ji Ummi Zee-Zee

-Tshowar jarumar Kannywood ta bayyana cewa, har yanzu tana raye bata mutu ba tukuna

- An gano labarin mutuwar ta baya a shafinta ta Instagram, kawarta ke ba da labarin mutuwar

- Sai dai a jiya, ta rubuta a shafin cewa bata mutu, kawai dai ta shiga wata doguwar suma ne

Tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Ummi Zee-zee ta leko Instagram biyi bayan jita-jitan mutuwar ta, ta ce tana raye daram ba ta mutu ba.

A makon da ya gabata ne aka shiga rudu da mamaki biyo bayan samun labarin da ya fito daga shafin na Instagram cewa ta rasu.

Sai dai tsohuwar jarumar ta ce ta shiga dogon suma ne ba mutuwa ba, wanda hakan ya sa kawarta wadda a lokacin tana gidanta ne ta yi tsammanin ta rasu bayan ta yi ta zuba mata ruwa amma ba ta farfado ba.

KU KARANTA: Hukumar haraji ta Kano ta garkame GTBank kan kin biyan haraji

Ban mutu ba, dogon suma na yi saboda tsananin rashin lafiya, in ji Ummi Zee-Zeenata
Ban mutu ba, dogon suma na yi saboda tsananin rashin lafiya, in ji Ummi Zee-Zeenata Hoto: ummizeezee
Asali: Instagram

A cewarta, “Ina mai ba ku hakuri dangane da labarin da kuka ji cewa na mutu. To da raina ban mutu ba.

“Kawai dai na yanke jiki na fadi ne a gidan wata kawata a Kaduna.To sai ta yi zaton na mutu ne saboda ta yi ta zuba min ruwa ban farfado ba.

“Shi ya sa ta bayyana wa duniya cewa na mutu sai da mijinta ya kaini asibiti ne aka duba, aka ce ban mutu ba.

“Saboda haka duk wanda ya nuna damuwarsa jin labarin, ina godiya da kaunarsa. Sai dai ina fama da rashin lafiya matuka domin ina fama da ciwon matsananciyar damuwa. Don haka ina bukatar addu’ar masoya,” inji Zee-Zee.

A kasan rubutun nata a Instagram, jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, wasu daga ciki har da jaruman fim na Kannywood.

Wani darakta a masana'antar Kanyywood Aminu S. Bono cewa ya yi, “Zango na uku ke nan, saura zango na hudu.”

Shi kuma Darakta Sheikh Isa Alolo cewa ya yi “Abin mamaki shi ne ita da take rude amma ba ta manta lambobin sirrin wayarki ba, shi ne ta bude wayarki ta shiga Instagram dinki ta yi rubutun, maimakon ta yi a nata shafin.

"Ko da yake ba abin mamaki ba ne ko ita ba ta da shafin Instagram. Allah Ya kare mu, Ya kare mana imaninmu,” inji shi.

KU KARANTA: JAMB ta zargi UniAbuja da ba da guraben shiga jami'a ba bisa ka'ida ba

A wani labarin daban, Fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Ta ce: “A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel