Masoya tun daga sakandare sun angwance bayan shekaru 15 suna soyayya
- Labarin soyayyar wani ango da amaryarsa ya bai wa jama'a da yawa mamaki
- Ma'auratan da suka angwance a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilu sun fara soyayya tun suna sakandare
- Sun rike amana tare da cigaba da soyayya har lokacin da suka shiga makarantun gaba da sakandare
Wasu ma'aurata 'yan Najeriya sun tabbatar da cewa soyayyar amana har a wannan zamanin akwai ta.
Ma'auratan sun angwance a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilu tun daga soyayyar da suka fara a 2006 lokacin suna makarantar sakandire.
A yayin taya su murnar aurensu, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Adams Philip Nathaniel, ya bada labarin yadda soyayyar ta fara.
KU KARANTA: Umarnin Ubangiji ne: Fasto yayi zanga-zanga kan mulkin Buhari da akwatin gawa
KU KARANTA: Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai
Adam yace amarya da angon masu suna Akoji da Ojochegbe, 'yan asalin jihar Kogi ne kuma sune daliban da aka fara yayewa a makarantar sakandire ta Ankpa dake jihar Kogi kuma sun kasance mazauna wuri daya tun a lokacin.
A yayin da suke makaranta, Akoji yana samun sabani da wasu 'yan ajinsu wadanda yake zargi da yunkurin raba shi da rabin ransa.
Ana haka, sai suka fada soyayya wacce har ta cigaba bayan sun shiga kwalejin horar da malamai ta yankin.
Babu kakkautawa 'yan Najeriya suka garzaya sashen tsokaci suka dinga tofa albarkacin bakinsu tare da taya su murna.
Victor Unewejo cewa yayi: "Wayyo Allah na!! Ka san labarinsu da kyau. Ina taya su murna da fatan samun albarka a aurensu."
Buoyant Saint Romzy cewa tayi: "Wannan abu yayi kyau"
A wani labari na daban, lamari ya dauka zafi tsakanin wasu 'yan kwamitin rikon kwarya na majalisar wakila a kan makamai, da shugaban sojin kasa, Laftanal janar Ibrahim Attahiru bayan bincike a kan siyan makamai na sojin Najeriya.
Lamarin ya juya yayin da shugaban sojin kasan ya ki kara bayani kan wasu takardu da ya mika gaban kwamitin inda yace su duba takardun da kansu domin babu wani karin bayani.
Shugaban sojin ya jaddada cewa bai dade da hawa kujerarsa ba don haka ba shi ke da hakkin yin magana a kan makaman da magabatansa suka siya ba, Channels Tv ta wallafa.
Asali: Legit.ng