Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai

Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce an zabe shi ne don ya bunkasa jihar ba don biyan albashi ba

- Ya furta hakan ne kwanaki kadan bayan ya sallami ma'aikatan kananun hukumomi 23 guda 4000

- Ya kara da bayyana cewa an zabe shi ne don gyara makarantu, asibitoci da gyaran jihar tare da samar da ayyuka

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce an zabe shi ne don bunkasa jihar ba don biyan albashi ba.

Hakan ya biyo bayan sallamar ma'aikata 4000 na kananun hukumomi 23 da suke jihar da gabatar musu da wasikun sallamar.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa an zabe shi ne don samar da damar ayyuka, gina makarantu da asibitoci, gyaran tituna da samar da ma'aikatu don samar da ayyuka na musamman.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje

Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai
Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

El-Rufai ya bayyana hakan a wata takarda wacce mai baiwa gwamna shawara na musamman, Muyiwa Adekeye ya sanya hannu, ya ce asusun gwamnati ya samu nakasu saboda ba a kara kudin shiga daga gwamnatin tarayya ba.

"A watan Nuwamban 2020, asusun jihar Kaduna yana da N162.9M bayan an biya albashi da samun N4.83bn daga FAAC, aka biya albashin N4.66bn," a cewarsa.

Gwamnatin ta bayyana abinda ake samu daga FAAC tun 2020, kamar yadda sauran jihohi, wadanda da kyar suke biyan albashi.

A cewarsa, "A watanni 6 da suka gabata, kudaden da ake kashewa sun kai 84.97% da 96.63% na kudaden da ake samu daga gwamnatin tarayya zuwa gwamnatin jihar Kaduna.

"A watan Maris na 2021, gaba daya a asusun jihar Kaduna saura N321m bayan an kammala kasafin jihar."

Takardar ta watan Maris na 2021, ta bayyana yadda ta samu N4.819b daga gwamnatin tarayya sannan ta biya N4.498b wanda hakan ya kai kaso 93% na kudin da yake shigowa asusun jihar.

KU KARANTA: Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta

A wani labari na daban, wani dalibin sakandare mai suna Philemon Igbokwe ya samu kyauta mai tsoka bayan ya mayar da wata waya da ya tsinta ga mai ita a Fatakwal, jihar Rivers.

Wani lauya mai suna Emma Okah, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 11 ga watan Afirilu, inda yace yaron ya tsinci wayar ne a bayin dakin taro da yaje.

Mr Okah ya baiwa yaron kyautar N50,000 yayin da wasu baki biyu suka baiwa yaron $500 da N50,000. Gaba daya dai yaron ya tashi da N340,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel