Umarnin Ubangiji ne: Fasto yayi zanga-zanga kan mulkin Buhari da akwatin gawa
- Wani babban faston Najeriya mai suna Archbishop Samson Benjamin ya yi zanga-zanga akan mulkin Buhari a ranar Lahadi
- Faston wanda aka fi sani da Jehovah Sharp sharp, ya yi zanga-zangar ne da akwatin gawa a kansa don nuna takaicinsa da mulkin Buhari
- Bishop din ya yi ikirarin cewa Ubangiji ne ya umarce shi da yin hakan don baya farinciki da shugabanci da halin da kasar nan take ciki
Wani faston Najeriya kuma mai kula da Resurrection Praise Ministry, Archbishop Samson Benjamin ya yi zanga-zanga akan mulkin Buhari a ranar Lahadi a Legas dauke da akwatin gawa a kanshi.
Faston wanda aka fi sani da Jehovah Sharp sharp, ya ratsa titunan Festac dauke da akwatin gawa a kansa.
Bishop din ya yi ikirarin cewa Ubangiji ne ya umarce shi da hakan saboda fushin da yake yi da shugabancin kasar nan.
Mai wa'azin ya bayyana yadda rayuwa ta kasance tsaye cak a 'yan shekarun nan.
KU KARANTA: Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta
"Tun daga 15 ga watan Satumba 2019 zuwa yanzu, ban sake cin abincin da wuta ta girka ba ko wani abu mai dadi, ina ta rokon Ubangiji akan halin da kasar nan take ciki.
"A cikin makon da ya gabata, ruhina ya tafi, ban sake magana da wani mutum ba kuma ban ga rana ba, wata ko sararin samaniya ba.
"Abinda kuka ga ina yi anan Ubangiji ne ya umarceni da yin hakan inda yace in dauki wata alama don in nuna wa shugabannin kasar nan.
"Ya ce in dauki akwatin gawa a kaina, don ba wani abin ado bane, abu ne wanda idan mutum ya mutu ake sanya shi."
Benjamin ya janyo irin sakon da aka sanar dashi inda yace ya ji ana ce masa: "Ka sanar da shugabannin da suke rike dukiyar al'umma wannan kasa mai albarka suna wahalar da talakawa cewa bana farin ciki da hakan."
Faston ya bukaci 'yan Najeriya dasu sanar da shugabanninsu gaskiya cewa Ubangijin da ya baiwa kasar nan albarka ya kuma basu shugabanci yana fushi dasu.
KU KARANTA: Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa
"Sai dai masu mulki sun zabi satar dukiyoyin al'umma don su killace wa kansu, hakan ne ya sanya na dauki akwatin gawa don in sanar dasu cewa Ubangiji yana fushi dasu, ba shugabannin siyasa kadai ba har na addinai da na gargajiya."
Da aka tambayeshi dalilin daya sanya bai kai akwatin gawar fadar shugaban kasa ba ya bayyana cewa Ubangiji bai umarceshi da yin hakan ba.
A wani labari na daban, 'yan ta'adda sun kaiwa kayan tallafi a Damasak, jihar Borno farmaki kamar yadda NRC ta tabbatar. Sai da suka saci na sata sannan suka bankawa sauran wuta a ma'ajiyarsu.
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, dama sun taba kai farmakin a karo na biyu kenan a arewa maso gabas, sannan karo na hudu kenan a Damasak da kewaye.
Darekatan NRC na Najeriya, Eric Batonon, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace ma'aikatan wurin guda 5 sun tsira.
Asali: Legit.ng