Jiragen Yaƙi shida daga Amurka Zasu iso Najeriya a watan Yuli, 2021 - Inji Fadar shugaban ƙasa

Jiragen Yaƙi shida daga Amurka Zasu iso Najeriya a watan Yuli, 2021 - Inji Fadar shugaban ƙasa

- Gwamnatin tarayya tace jirage shida daga cikin 12 da ta siya daga ƙasar Amurka zasu iso Najeriya a tsakiyar watan Yuli, don ƙara ma rundunar Sojin sama ƙarfin gwuiwa.

- Babban mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Garba shehu, shine ya bayyana haka

- Hakanan kuma Garba Shehu ya ce a yanzun haka akwai matuƙan jirgin sama guda 14 dake cigaba da amsar horo

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa shida daga cikin jiragen yaƙi 12 da gwamnatin tarayya ta siyo daga Amurka ƙirar 'Super Tucano' zasu iso gida Najeriya a tsakiyar watan Yuli, 2021.

KARANTA ANAN: Shekaru 7 Kenan, Muna Buƙatar mu haɗu da 'ya'yan mu Kafin mu mutu, Iyayen Ɗaliban Chibok Sun roƙi FG

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da babban mai taimaka ma shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar.

Garba Shehu ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sada zumunta wato Tuwita inda ya ce kashin farko na jiragen zasu iso ne a tsakiyar watan Yuli, 2021.

Mr. Shehu ya ce ragowar jiragen shida, zasu biyo baya bada jimawa ba bayan isowar kashin farko a tsakiyar watan Yuli.

Jiragen Yaƙi shida daga Amurka Zasu iso Najeriya a watan Yuli, 2021 - Inji Fadar shugaban ƙasa
Jiragen Yaƙi shida daga Amurka Zasu iso Najeriya a watan Yuli, 2021 - Inji Fadar shugaban ƙasa Hoto: @Garshehu
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Hakanan kuma Garba shehu ya ƙara da cewa akwai matuƙan jirgi 14 da gwamnati ta tura, waɗanda a yanzun haka suna cigaba da amsar horo a Moody Airforce Base Georgia.

Wannan matakin da gwamnati ta ɗauka na ƙaro ma rundunar soji kayan aiki zai taimaka matuƙa wajen yaƙin da take da matsalar tsaro a ƙasar nan.

A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa 6 Zasu haɗa ƙarfi-da-ƙarfe Wajen yaƙar yan Ta'adda a Yankunan su

Wasu gwamnoni shida daga Arewa zasu haɗa hannu domin kawar da ta'addanci a jihohin su.

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ne ya bayyana haka amma bai faɗi sunayen sauran gwamnoni biyar ɗin da zasu yi haɗakar da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262