Ku mayar da hankali kan rashin tsaro, ba sanya dokar hijabi ba, CAN ga majalisar wakilai

Ku mayar da hankali kan rashin tsaro, ba sanya dokar hijabi ba, CAN ga majalisar wakilai

- Kungiyar CAN ta caccaki majalisar wakilai kan kudurin dokar sanya hijabi ga Musulman Najeriya

- CAN ta ce maimakon wannan kuduri, kamata yayi majalisar ta maida hankali kan magance tsaro

- Ta kuma roki majalisar da ta yi kokarin nemo hanyar samar da ayyuka ga matasa don magance ta'addanci

Wani dan majalisar wakilai, Mista Musa Saidu Abdullahi, da ya dauki nauyin kudirin da ke neman tilasta sanya hijabi ga mata Musulmai a wuraren taron, ranar Talata, ya gana da shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya, inda ya yi bayanin dalilan yanke shawarar.

Kungiyar kiristocin, ta nuna rashin jin dadinta game da kudirin, tana mai cewa tuni Najeriya tana da dokoki da za su kare ‘yan kasa daga kowane irin nuna bambanci, ciki har da addini.

Don haka, kungiyar ta bukaci wakilin, da kuma mambobin Majalisar Dokokin da su mai da hankali kan manyan matsalolin kasar, ciki har da rashin tsaro, The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Matar gwamnan Zamfara ta tabbatar da nadin membobin Miyetti Allah 20 a gwamnati

Ku mayar da hankali kan rashin tsaro, ba sanya dokar hijabi ba, CAN ga majalisar wakilai
Ku mayar da hankali kan rashin tsaro, ba sanya dokar hijabi ba, CAN ga majalisar wakilai Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Abdullahi, wanda ke wakiltar mazabar Bida/Gbako/Katcha ta Tarayya a Jihar Neja, ya dauki nauyin Dokar Nuna Bambanci (Haramtawa da Hanawa) Dokar 2021, wacce ta wuce tattaunawa ta daya da ta biyu.

A jawabinsa Abdullahi ya ce, “Ina ganin matsalar da ta zama babban kalubale kuma mun guji hakan a tsawon shekaru. Batun nuna bambancin addini ne. Don haka, mun zo da wata shawara don magance wariyar addini a kasar nan.”

Shugaban na CAN ya ce, “Wannan kudirin karamin abu ne; ya kamata mu sanya shi a matsayin abu mai mahimmanci wanda duk mai hankali zai karanta ya ce 'wannan yana ciyar da kasar Najeriya gaba.'

"Don Allah, honarabul, ina kira gare ku da abokan aikin ku da ku taimaka mana ku nemo hanyar kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.

“Alamu ba sa nuna cewa muna son kawo karshen sa. Muna jin kishin-kishin cewa ana karkatar da kudin da aka ware don tsaro.

"Idan kun ga irin jarin da za mu rasa saboda rashin tsaro… Ko yawon bude ido na addini yana da matukar wahala yanzu saboda rashin tsaro.”

Ya kara da cewa, “Muna bukatar samar da ayyukan yi. Rashin aikin yi ne ke haifar da rashin tsaro saboda 'yan ta'adda da 'yan bindiga suna iya daukar mutane cikin sauki, ba tare da an sarrafa su ba. Suna ba su kudi kadan, sun gamsu. Amma gwamnati ba ta yin hakan.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bukaci a basu buhunan shinkafa a matsayin fansa a Abuja

A wani labarin, Bishop din Cocin Katolika na Sakkwato, Rev. Matthew Kukah, ya ce zai ci gaba da addu’a wata rana Musulmai ko za su gina wa Kiristoci coci.

Mista Kukah ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ake kaddamar da rukunin gidaje 86 tare da coci da masallaci ga 'Yan Gudun Hijira a kauyen Sangere-Marghi da ke karamar Hukumar Girei a Jihar Adamawa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa musulmai da kirista duka sun ci gajiyar gidajen da Rev. Stephen Dami Mamza, Bishop din Cocin Katolika na Yola ya gina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel