Ganduje ya gina wa Almajirai makarantun tsangaya uku a jihar Kano

Ganduje ya gina wa Almajirai makarantun tsangaya uku a jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da makarantun tsangaya guda uku a jihar

- Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar ne ya sanar da hakan a ranar Talata a gidan gwamnati

- Ganduje ya ce an kafa wannan makarantun ne bayan haramta almajiranci a jihar saboda almajiran jihar su samu wurin karatu na addini da boko

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kafa makarantun Tsangaya uku a jihar domin gwamutsa karatun almajiranci da na boko a jihar, The Punch ta ruwaito.

Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya sanar da hakan yayin rabar da kayayyakin koyarwa da kaddamar da jaridar "Teen Trust" a gidan gwamnati a Kano a ranar Talata.

Ganduje ya gina wa Almajirai makarantun tsangaya uku a jihar Kano
Ganduje ya gina wa Almajirai makarantun tsangaya uku a jihar Kano. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Ya ce an kafa makarantun ne bayan gwamnatin jihar ta haramta almajiranci ta kuma mayar da almajiran da ke jihar zuwa jihohinsu na ainihi.

"An gina makarantun tsangaya uku domin almajiran jihar Kano da wadanda aka dawo mana da su daga wasu jihohin.

"Kawo yanzu mun zabi almajirai 100 domin su shiga makarantun, mun samar musu da kayayyakin karatu da tufafin makaranta," in ji shi.

Ganduje ya ce gwamnatin jihar za ta cigaba da bada ilimi kyauta a jihar tare da shigar da makarantun almajirai cikin makarantun zamani domin bawa yara damar samun ilmin addini da na boko a lokaci guda.

KU KARANTA: El-Rufa'i ya umurci cocin RCCG ta cigaba da baza rassa a faɗin jihar Kaduna

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin wasu malaman frimari wadanda ba su da shaidar karatun malanta na NCE su tafi su yi karatun domin inganta aikinsu.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: