Boko Haram ta nemi N30m kafin ta sako mutum 30 da ta sace a Adamawa

Boko Haram ta nemi N30m kafin ta sako mutum 30 da ta sace a Adamawa

- Wasu mutanen garin Kwapre a Adamawa sun ce Boko Haram ta nemi a biya N30m kudin fansa kafin ta sako mutum 30 da ta sace

- Amma shugaban karamar hukumar Hong na jihar Adamawa, James Pukama ya ce bai san da maganar kudin fansar ba

- Kazalika, adadin mutanen da suka rasu sakamakon harin ya karu daga bakwai ya kai 10 yayin da dama suna asibiti suna jinya

Adadin mutanen da suka suka mutu sakamakon harin da Boko Haram ta kai garin Kwapree a karamar hukumar Hong na jihar Adamawa ya kai 10.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu mazauna garin a ranar Litinin suka ce yan ta'addan Boko Haram sun kira su suna neman a biya Naira Miliyan 30 kafin su sako mutum 30 d suka sace a yayin harin da suka kai garin, rahoton The Punch.

Boko Haram ta nemi N30m kafin ta sako mutum 30 da ta sace a Adamawa
Boko Haram ta nemi N30m kafin ta sako mutum 30 da ta sace a Adamawa. Hoto: @channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

Shugaban karamar hukumar, James Pukama, a ranar Litinin yace yayin ziyarar da kakakin majalisar jihar Adamawa ya kai, adadin wadanda suka mutu ya karu daga bakwai zuwa 10 bayan gano wasu gawarwaki.

Idan za a iya tunawa an ce yan Boko Haram ne suka kai harin a Kwapree inda suka kashe mutum bakwai sannan fiye da mutum 5000 suka tsere daga gidajensu.

Wasu mazauna Kwapre da suka ce ba su son a ambaci sunayensu sun shaidawa The Punch cewa wadanda suka kai musu harin a ranar Lahadi sun kira sun nemi a biya fansar Naira Miliyan 30.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

Amma shugaban karamar hukumar ya ce bai san batun neman biyan kudin fansar ba.

Ya ce, "Babu wani maganar kudin fansa. A jiya, mutane bakwai aka tabbatar sun mutu, yau adadin ya kai 10, yayin da mutum 53 da ke asibiti suna nan ana musu magani."

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel