Yan Bindiga sun kai hari wata Kasuwa a jihar Neja, sun kashe yan Bijilanti Biyar

Yan Bindiga sun kai hari wata Kasuwa a jihar Neja, sun kashe yan Bijilanti Biyar

- Wasu yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kasuwa da kuma wasu ƙauyukan dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja

- Biyar daga cikin jami'an tsaron sa kai sun rasa rayuwar su a lokacin da suka fafata da maharan, da yawa kuma sun jikkata

- Wani matashi mai kishin yankinsa ya bayyana cewa yanzun irin wannan harin ya zama ruwan dare a ƙaramar hukumarsu

Wasu yan bindiga sun kai hari a wata kasuwa inda suka kashe jami'an tsaron sa kai (Vigilantes) guda biyar suka kuma jikkata wasu da yawa, Dailytrust ta ruwaito.

Rahotannin sun tabbatar da cewa 5 daga cikin tawagar yan bijilanti sun rasa rayukan su, wasu kuma da yawa sun jikkata a harin da yan bindigar suka kai kasuwa da wasu yankunan ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja.

KARANTA ANAN: Yanzu Yanzu: Gwarazan Sojoji na can suna fafatawa da yan bindiga a iyakar Ebonyi Da Benuwai

Rahotannin sun bayyana yan bindigar sun kai hari a ƙauyuka kamar; Beri, Beri-Kago, Gatawi,Kini, Bmada da sauran kauyukan dake kusa da nan a ƙaramar hukumar.

Wani matashi mai kishin yankinsa, Sani Abubakar Yusuf Kokki, ya tabbatar da kai harin inda ya ce irin waɗannan hare haren sun zama ruwan dare a yankin.

Ya kuma ƙara da cewa ana yawan kai irin waɗannan harin a yankunan ƙaramar hukumar Shiroro kuma ba wani ɗauki da suke samu daga masu ruwa da tsaki.

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga sun kai hari wata Kasuwa a jihar Neja, sun kashe yan Bijilanti Biyar
Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga sun kai hari wata Kasuwa a jihar Neja, sun kashe yan Bijilanti Biyar Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar matashin:

"Da safiyar yau, yan bindiga da yawa sun farmaki wani adadi na ƙauyukan a Gurmana dake ƙaramar hukumar Shiroro."

"Biyar daga cikin jami'an mu na sa kai sun rasa rayuwarsu a ɗauki ba daɗin da suka yi da yan bindigar."

KARANTA ANAN: Dr. Isa Ali Pantami ya yi martani kan rubutun da aka yi akansa na hannu a Boko Haram

"A ya yin harin, mutane da yawa waɗanda suka haɗa da jami'an sa kai sun jikkata wasu an harbe su, anji ma wasu munanan raunuka, Sannan kuma yan bindigar sun yi awon gaba da wasu dayawa zuwa inda ba'a sani ba."

Sani Abubakar ya ƙara da cewa abun takaicin shine babu wani jami'in tsaro a gaba ɗaya yankin da aka kai harin.

Sai dai an tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar ta Neja amma ba'a same shi ba bare ya tofa albarkacin bakinsa a kan abinda ya faru.

A wani labarin kuma Bamu san an buga sabbin Kuɗi a watan Maris ba, CBN da Ma'aikatar kuɗi sun maida Martani

Babban Bankin Najeria CBN ya ce shi baisan da zancen buga sabbin kuɗi na kimanin biliyan N60bn da ake cewa gwamnati ta yi a watan Maris ba

A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa gwamnati bata da kuɗi, saida aka buga sabbi na 60 biliyan don rabawa a matakan gwamnati a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel