Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar mata masu zaman kansu mazauna jihar

Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar mata masu zaman kansu mazauna jihar

- Gwamnatin jihar Bauchi za ta gudanar da kidayar mata masu zaman kansu don sanin asalin yawansu

- Kwamishinan Hisbah da harkokin shari'ar jihar ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tattaunawa da matan

- A cewarsa zasu gudanar da wannan kidayar ne don sanin yadda zasu kawo karshen wannan sana'ar tasu mai hatsari

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce zata gudanar da kidayar mata masu zaman kansu da suke fadin jihar don sanin asalin yawansu a jihar, Premium Times ta wallafa.

Aminu Balarabe-Isah, kwamishinan Hisbah da Shari'a ya bayyana hakan a Bauchi ranar Litinin yayin tattaunawa da mata masu zaman kansu na jihar.

A cewarsa, samun asalin yawansu don sanin yadda zasu bullo wa lamarin zai taimaka wurin kawo karshen wannan mummunar sana'a.

KU KARANTA: Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa

Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar karuwai mazauna jihar
Gwamnatin Bauchi za ta yi kidayar karuwai mazauna jihar. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Isah ya bayyana hakan inda yace gwamnatin jihar zata samar da shirin basu jari don fara kananun sana'o'i.

A cewarsa, sun gudanar da wannan binciken inda suka gane cewa mata masu zaman kansu sun dauki karuwanci a matsayin sana'a sakamakon jahilci, fatara ko kuma wahalhalun kishiyoyin uwayensu.

Ya kara da bayyana cewa rushewar gida yana janyo yara mata su fara tunanin fara karuwanci, don haka zasu tabbatar sun mayar dasu hannun iyayensu.

Kwamishinan ya bayyana yadda yake a shirye da ya aurar da wadanda suka samu mazajen aure amma basu da halin yin hakan.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

Hafsatu Azare, mai magana da yawun mata masu zaman kansu ta bayyana yadda duk suka shirya tsaf don daina sana'ar karuwanci matsawar suka samu sana'o'in da zasu tallafa wa kawunansu.

A wani labari na daban, yayin da kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa ba a samu ganin watan Ramadan ba ranar Lahadi, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan a ranar Litinin.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a da dama, sai dai Legit.ng ta samu zantawa da Shehin Malami Ustaz Abu Jabir wanda aka fi sani da PenAbdul.

Malamin ya bayyana cewa kasar nan tana la'akari da ganin watanmu ne ba kasar Saudia ba. Koda kasar Saudi Arabia tace bata ga wata ba, Najeriya za ta duba watan, idan duk ba a gani ba, toh an yi tarayya a rashin ganin watan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel