Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa

Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa

- An baiwa dalibin sakandare kyautar kudi bayan ya mayar da wata waya da ya tsinta ga mai ita a Fatakwal, jihar Rivers

- Wani lauya, Emma Okah ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 11 ga watan Afirilu

- Ya bayyana yadda yaron ya tsinci wayar a bayin baki dake dakin taron wani biki, bayan ya mayar aka bashi kyautar N340,000

Wani dalibin sakandare mai suna Philemon Igbokwe ya samu kyauta mai tsoka bayan ya mayar da wata waya da ya tsinta ga mai ita a Fatakwal, jihar Rivers.

Wani lauya mai suna Emma Okah, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 11 ga watan Afirilu, inda yace yaron ya tsinci wayar ne a bayin dakin taro da yaje.

Mr Okah ya baiwa yaron kyautar N50,000 yayin da wasu baki biyu suka baiwa yaron $500 da N50,000. Gaba daya dai yaron ya tashi da N340,000.

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke soji 3 da wasu 'yan ta'adda a harin Boko Haram a Damasak

Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa
Dalibi ya samu kyautar N340,000 daga mutumin da ya tsinta wayarsa ya mayar masa. Hoto daga lailasnews.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari ma'adanar kayan tallafi, sun kone wurare a Borno

"Yaron nan da muka dauki hoto tare sunansa Philemon Igbokwe, kuma dalibin FGC Rumuokoro, PH dake jihar Rivers ne. Bashi da waya ko karama.

"Jiya ne na jagoranci wani biki na Mr. Victor Emma Woke daga garin Elele da matarsa Joy daga Eleme a dakin taro na Exquisite (Eliozu), G.U. Titin Ake, PH," yace.

Philemon ya bayyana yadda gaskiya da amana suka yi karanci amma duk da haka yaro ya tsinci sabuwar waya a bayi. Shugaban taron ya bayyana yadda mutane suka yaba da hankali da gaskiyar yaron.

"Na baiwa yaron kyautar N50,000, Hon. Josiah Olu ya bashi N50,000 sai Dr John Bosco ya bashi $500. Gaba daya Philemon Igbokwe zai tafi da kyautar N340,000, wanda da ya sayar da wayar bata wuce N40,000 ba.

"Ina taya Philemon da iyayensa murnar taso da yaro mai nagarta a kasar nan. Muna yi wa Philemon fatan samun daukaka shi da iyayensa."

A wani labari na daban, Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce zanga-zangar EndSARS ta zalincin 'yan sanda, Boko Haram da sauran matsalolin tsaro suna aukuwa ne sakamakon fatara da rashin adalci.

Yayin da Rochas yake amsar jinjinar "Abokin mutanen Ibadan na musamman" da CCII suka gabatar masa a ranar Asabar ya bayyana hakan.

Jinjinar da Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadan ya baiwa Rochas bisa kula da kokarinsa na tallafawa ilimin yaran talakawa da marayu a shirinsa na bayar da ilimi kyauta a makarantun Ibadan, jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel