Gwamnan Bauchi Ya amince ya biya ma ɗaliban Sakandiren jihar kuɗin JAMB da NECO

Gwamnan Bauchi Ya amince ya biya ma ɗaliban Sakandiren jihar kuɗin JAMB da NECO

- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya amince ya biya ma ɗalibn dake ajin ƙarshe a sakandire kuɗin jarabawar JAMB da NECO

- Gwamnan ya ce za'a biya ma ɗaliban sakandiren ne waɗanda suka cike sharuɗɗan da gwamnatin ta kafa

- Hakanan kuma ta ce duk ɗalibin da ya cancanci a biya masa JAMB to dole sai ya mallaki lambar NIN

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya mince ya biya ma ɗalibai 3,810 kuɗin jarabawar share fagen shiga babbar makarantar gaba da sakandire JAMB.

Gwamnan ya amince a biya ma ɗaliban da suka fita da sakamakon 'A' ko 'B' kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku

Kwamishinan Ilimi na jihar, Aliyu U. Tilde, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin.

Jawabin ya ce: "Gwamnan jihar ya amince da biya ma ɗaliban dake ajin ƙarshe a babban sakandire su 1,751 kuɗin jarabawar NABTEB. Hakanan gwamnan ya amince da biya ma ɗalibai 499 kuɗin zana jarabawar NBAIS."

"Shekara mai zuwa duk wanda za'a biya mawa sai an gwada shi anga ya cancanta tukunna." inji gwamnan.

Hakanan gwamnan ya ce gwmnatinsa zata biya ma ɗaliban jihar kuɗin jarabawar NECO kamar yadda ta saba ga waɗanda suka ci A, B ko C a gwajin da aka musu.

Gwamnan Bauchi Ya amince ya biya ma ɗaliban Sakandiren jihar kuɗin JAMB da NECO
Gwamnan Bauchi Ya amince ya biya ma ɗaliban Sakandiren jihar kuɗin JAMB da NECO Hoto: @senbalamuhammed
Asali: Twitter

Idan aka haɗa kuɗaɗen da ɗaliban zasu laƙume a shekara ɗaya sun kai kimanin N18,580,550.00.

KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya

Gwamnatin ta ƙara jaddada cewa babu wata hukumar dake da alhakin shirya jarabawa da take bin gwamnatin bashin ko sisi.

A jawabin kwamishinan ilimin jihar ya ce duk ɗalibin da ya cika matakin da za'a biya masa JAMB dole ya kasance ya mallaki lambar NIN.

Ya ƙara da cewa an yi duk wani shirye-shiryen da ya kamata don ganin an biyawa ɗaliban da suka cancanci zana JAMB a kusa da hedkwatar ƙaramar hukumar su.

Kwamishinan yace za'a tura wa kowacce makaranta jerin sunayen waɗanda gwamnatin zata biyama JAMB ɗin ta hanyar saƙon karta kwana (E-Mail).

A wani labarin kuma Ganduje Ya ƙona kayan Abinci da suka Lalace na 90 miliyan saboda Ramadan

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje, ta lalata kayayyakin abinci da na sha da lokacin amfanin su ya wuce.

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ce ta bayyana haka ranar Litinin bayan gudanar da aikin a wasu kasuwannin jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel