Zuwan Ramadan: Ganduje Ya ƙona kayan Abinci da suka Lalace na 90 miliyan saboda Ramadan

Zuwan Ramadan: Ganduje Ya ƙona kayan Abinci da suka Lalace na 90 miliyan saboda Ramadan

- Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje, ta lalata kayayyakin abinci da na sha da lokacin amfanin su ya wuce

- Hukumar kula da lafiya a matakin farko ce ta bayyana haka ranar Litinin bayan gudanar da aikin a wasu kasuwannin jihar

- Ta ƙara da cewa an lalata kayayyakin ne saboda umarnin da kotu ta bayar na yin hakan, da kuma zuwan Watan Azumin Ramadana

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano, ta bayyana cewa ta lalata kayayyakin abinci da lokacin amfani da su ya wuce na 90 miliyan.

KARANTA ANAN: Kuɗin Makamai: EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi

Hukumar tace ta lalata kayan abincin ne a wasu ƙasuwanni dake faɗin jihar kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai magana da yawun hukumar, Mr Maikudi Marafa, ya yi a ranar Litinin.

Ta ƙara da cewa sakataren hukumar, Dr Tijjani Husain, wanda daraktan kula da lafiyar muhalli, Alhaji Usman Rabiu, ya wakilta, shine ya jagoranci tawagar da ta lalata kayayyakin.

A jawabin Husain yace: "An gudanar da wannan aikin ne saboda kare lafiyar al'umma daga kamuwa da cututtukan da kayan ka iya haifarwa, musamman saboda zuwan watan Azumin Ramadan."

Zuwan Ramadan: Ganduje Ya ƙona kayan Abinci da suka Lalace na 90 miliyan saboda Ramadan
Zuwan Ramadan: Ganduje Ya ƙona kayan Abinci da suka Lalace na 90 miliyan saboda Ramadan Hoto: @KanostateNG
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami

Ya kuma bayyana cewa an lalata kayayyakin ne bayan kotu ta bada umarnin yin hakan.

Hakanan, hukumar ta gargaɗi mutanen jihar Kano da su kasance a ankare don guje ma amfani da kayayyakin da lokacin amfanin su ya ƙare.

Daga cikin kayayyakin da aka lalata akwai; Magunguna, hodar yin buredi, kayan sanyi (Minerals) da dai sauran su.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar na ankare da kayayyakin abinci da na sha waɗanda lokacin amfanin su ya wuce tun wata ɗaya da ya gabata.

A wani labarin kuma Daga ƙarshe, shugaban Sojoji COAS ya bayyana a gaban yan majalisa

A kwanakin baya dai kwamitin ya aike da katin gayyata ga Shugaban sojin da kuma gwamnan babban bankin Najeriya amma basu sami zuwa ba

Kwamitin ya aike da katin gayyata ga mutanen biyu ne dan suzo amsa tambayoyi kan yadda aka yi da kuɗin makamai, idan an siya ina aka kaisu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel