Dalilin da ya sa farashin Siminti ya tashi, Kamfanin Dangote

Dalilin da ya sa farashin Siminti ya tashi, Kamfanin Dangote

- A shekarar 2020 farashin Siminti ya tashi daga N2,600 zuwa N3500-N4000

- Har yanzu farashin bai koma yadda yake ba yayinda yan Najeriya ke kokawa

- Wasu sun ce farashin simintin Dangote ya yi arha a wasu kasashen Afrika fiye da Najeriya

Kamfanin Simintin Dangote ya bayyana farashin da yake sayarwa yan kasuwar Siminti daga masana'antunsa dake Obajana, Gboko, da Ibese.

Dirkatan Kamfanin na shirye-shirye da manyan ayyuka, Devakumar Edwin, ya bayyana hakan a jawabin da ya baiwa manema labarai ranar Talata.

A cewar Devakumar, N2,450 Dangote ke sayarwa yan kasuwar buhun Siminta a Obajana da Gboko, sannan N2,510 a masana'antar Ibese.

Amma a binciken da Legit.ng Hausa tayi, farashin Siminti a Kaduna da Abuja na tsakanin N3,300 to N3,500.

KU DUBA: Ustaz Abu Jabir PenAbdul: Me ake nufi da niyya, kuma ya ake yin niyyar azumin Ramadan?

Dalilin da ya sa farashin Siminti ya tashi, Kamfanin Dangote
Dalilin da ya sa farashin Siminti ya tashi, Kamfanin Dangote

KU KARANTA: Wasu fa'idodi 15 dake tattare da watan Ramadana da Azumi, Shaykh Muhammad Bin Uthman

Devakumar ya ce farashin Siminti ya tashi ne sakamakon yawan bukatar da rikicin annobar COVID-19 ya haifar.

"Ba za'a tsame Najeriya dake cikin rikicin sauye-sauye da ya haifar da tsadar kayayyakin aiki a masana'antu ba," yace.

"Domin ganin cewa an samu isasshen Siminti a gida, sai da muka daina fitar da Suminta kasashen waje kuma munyi asarar daloli sakamakon haka."

Ya ce kamfanin Dangote ya farfado da masana'antar dake Gboko bayan rufeshi shekaru hudu da suka gabata kuma kamfanin na asara ne ta hakan.

"Mun yi dukkan wannan ne don tabbatar da cewa mun samar da isasshen Siminta cikin kasar," ya kara.

"Kusan kashi 50% na abubuwan da muke siya na da alaka da Dalar Amurka, saboda haka farashin yawancin abubuwa masu muhimmanci irinsu iskar Gas, gypsum, buhuhuna, da kaya, ya tashi saboda faduwar darajar Naira da kuma karin kudin harajin VAT."

Ya ce abinda kamfanin yayi kawai shine kara kudin jigilar Siminti saboda tashin farashin mai, kayayyakin mota dss.

A bangare guda, Kamfanin BUA ya mayar da martani kan ikirarin kamfanin Dangote da kamfanin Flour Mill cewa matatar sukarin BUA dake garin Fatakwal matsala ce ga kamfanonin sukari a Najeriya.

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da shugaban Flour Mill, John Coumantaros, sun aike wasika ga Ministan kasuwanci da masana'antu inda suka tuhumi matatar sukarin BUA na saba tsarin sukari na Najeriya (NSMP).

Tsarin NSMP wani shiri ne da aka yi a 2013 na tabbatar da cewa Najeriya ta samu isasshen sukari da zai isa al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel