Wasu fa'idodi 15 dake tattare da watan Ramadana da Azumi, Shaykh Muhammad Bin Uthman

Wasu fa'idodi 15 dake tattare da watan Ramadana da Azumi, Shaykh Muhammad Bin Uthman

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa'ad, ya umurci daukacin al'ummar Musulmi su tashi da azumin watan Ramadana ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021.

Babban Malami, Shaykh Muhammad Bin Uthman, ya bayyana wasu fa'idoji 15 dake cikin wannan sabon wata da kuma ibadan da za'a gabatar a ciki.

Ga jerin fa'idojin da Malamin ya lissaffo:

1- Bautar Allaah, wato yin azumin bautar Allaah ne, karanta Suurah ta 2:183. Mafi girman fa’idah ga mumini kuwa shi ne bauta ma Allaah.

2-Babu wani wata da Allaah Madaukaki Ya kebe da saukar da mafificin littafinSA in ba Ramadaan ba(Q2:185)

3-Yawan karanta da kuma tilawar al-Qur’aani maigirma. Babu wani wata da a ke karanta al-Qur’aani maigirma da yawa irin watan Ramadaan.

4-Samun dare wanda ya fi wata dubu wajen falala da al-Khairi wato daren Laylatul Qadri, al-Qur’aani 97:3 (wato wanda ya dace da yin Ibaadah cikin wannan dare, tamkar ya yi ibadar shekara tamanin (80) ne!

5-Kukkulle kofofin Wuta da kuma bubbude kofofin al-Jannah, wato ishara ga yawaitar Rahmah da kuma hanyoyin samunta da kuma tsukewar kofofin Azaba

6-Yawaitar tsayuwar dare wadda ba’a samun haka in ba a watan Ramadaan ba.

7-An fi samun yawan ciyar da dukiya kan hanyoyi na alkhairi a Ramadaan sama da sauran watanni.

8-Majalisan bayani da kuma fassara al-Qur’aani maigirma sun fi yawaita a Ramadaan sama da ragowar watanni.

KU DUBA: Ustaz Abu Jabir PenAbdul: Me ake nufi da niyya, kuma ya ake yin niyyar azumin Ramadan?

Wasu fa'idodi 15 dake tattare da watan Ramadana da Azumi, Shaykh Muhammad Bin Uthman
Wasu fa'idodi 15 dake tattare da watan Ramadana da Azumi, Shaykh Muhammad Bin Uthman Hoto: Shaykh Muhammad Bin Uthman
Asali: Facebook

KU KARANTA: Fara azumin kafin sanarwan Sarkin Musulmi sabawa Manzon Allah ne, Ustaz Abu Jabir

9-A dalilin watan Ramadaan, musulmin Duniya gaba daya kan samu wani yanayi na karin hakuri ga barin ci da sha da kuma dangogi na sha’awa.

10- Ibaadar I’tikaafi-wadda Ibaada ce mai matukar romo da tsoka- a watan Ramadaan ne tafi kankama

11-Akwai wata kofa mai suna ar-Rayyaan masu azumi kadai ke shiga al-Jannah ta cikinta (Allaah KA sa muna cikinsu)- Hadiithin Bukhaary da Muslim. Ibaadar da ke ba mutum cancantar shiga al-Jannah ta wannan kofa ai a watan Ramadaan tafi bayyana kuma wadda take daya daga cikin shika-shikan Musulunci.

12- Yana daga cikin falalar watan Ramadaan cewa yin ‘Umrah a Ramadaan na daidai da Hajji tare da Manzon Allaah- sallal Laahu ‘alayhi wa sallama.

وعنِ ابنِ عباسٍ، رضي اللَّه عنهُما، أنَّ النَّبيَّ ﷺ قَالَ: عُمرَةٌ في رمَضَانَ تَعدِلُ حجة أَوْ حَجَّةً مَعِي متفقٌ عليهِ

13-Bashin bakin mai azumi a wajen Allaah ya fi al-Miski kamshi(Bukhaary da Muslim). Watan Ramadaan shi ne kan gaba wajen samar wa Muminai wannan garabasa.

14-Sanya miyagun aljannu da ibilisai cikin sarka da dakawrori da sarkoki a daren farko na Ramadaan

(Ibnu Khuzaimah da Tirmidhy da Nasa’iy da Ibnu maajah kuma sahiihi ne)

15-Tace jini da kuma habaka lafiya da ke tattare da Azumi.

Da sauransu domin ire-iren wadannan darajoji da falala na Ramadaan na da yawa.

ALLAAH, KA NUNA MANA RAMADAAN KUMA KA BAMU IKON AZUMTARSA YANDA YA DACE.

_*Shaykh Muhammad Bin Uthman*_

Asali: Legit.ng

Online view pixel