Najeriya na cikin tsaka mai wuya, Muna Buƙatar Addu'a, Inji gwamnan Lagos
- Gwmamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya ce ƙasar mu Najeriya na tangal-tangal, muna buƙatar addu'a sosai daga bakin malamai
- Gwamnan ya faɗi haka ne a wajen taron lakca da aka shirya a jihar saboda zuwan watan Ramadan wanda musulmi ke azumi a cikinsa
- Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan harkokin cikin gida na jihar ya yi kira ga musulmai su ƙara dagewa da ibada kuma su saka Lagos da kuma Najeriya baki ɗaya
Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira ga malamai da su saka Najeriya cikin addu'a saboda ƙasar na tangal-tangal kamar yadda PM News ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Badaƙalar Kuɗin Makamai: Daga ƙarshe, shugaban Sojoji COAS ya bayyana a gaban yan majalisa
Gwamnan ya ce Najeriya na neman zuwa ƙasa saboda ƙaruwar matsalolin tsaro da ya bai-baye ta.
Sai dai Gwamna Sanwo-Olu ya ce ƙasar na buƙatar addu'an neman dawwamammen zaman lafiya cikin gaggawa.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Dr Kadir Hamzat, ya wakilta a wajen lakcar azumin watan Ramadana na shekarar 2021 a gidan gwamnati, ya ce Najeriya na matuƙar buƙatar addu'a.
KARANTA ANAN: Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami
"Ya kamata mu dage da addu'a sosai domin ƙasar mu bata da tabbas, tana tangal-tangal, Allah ya amshi addu'ar mu." inji gwamnan.
A jawabin maraba da kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Lagos, Prince Anofiu Elegushi yayi, ya ce:
"Azumin watan Ramadan umarni ne daga Allah kamar yadda littafi mai tsarki Alƙur'ani ya faɗa a sura ta biyu, aya ta 183 'Ya ku waɗanda suka yi Imani, mun wajabta azumi akanku kamar yadda muka wajabatashi akan waɗan da suka zo kafin ku, ko zaku samu tsoron Allah."
"Kamar yadda kowa ya sani, shekarar data gabata a dai-dai wannan lokacin, duniya ta shiga cikin ruɗani saboda ɓarkewar annobar COVID19."
"Wadda ta tilasta ma kasashe da dama saka dokar kulle, wanda hakan yasa ba damar yin taro kamar wannan da muke yi yanzun."
"Saboda ya zama wajibi mu gode ma Allah bisa nasarar da ya bamu wajen yaƙar wannan cutar duk da illar da ta yi mana." inji Elegusi.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga musulmai da su ƙara dagewa wajen aikin ibada a watan Ramadana, kuma su saka jihar Lagos da kuma Najeriya baki ɗaya a cikin Addu'o'insu.
A wani labarin kuma CBN ya ce bashi da labarin an buga sabbin kuɗi na kimanin biliyan 60 a watan Maris
Babban Bankin Najeria CBN ya ce shi baisan da zancen buga sabbin kuɗi na kimanin biliyan N60bn da ake cewa gwamnati ta yi a watan Maris ba
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa gwamnati bata da kuɗi, saida aka buga sabbi na 60 biliyan don rabawa a matakan gwamnati a watan Maris.
Asali: Legit.ng