‘Yan Boko Haram sun kai hari, sun kashe mutane a ofishin Majalisar dinkin Duniya a Borno
- Boko Haram sun yi mummunan ta’adi a Damasak a karamar hukumar Mobbar
- ‘Yan ta’addan sun kashe Bayin Allah da wasu jami’an sojoji uku a ranar Asaba
- Mayakan na Boko Haram sun kona ofisoshi da motocin kungiyoyin kasar waje
Mutane akalla shida aka kashe, sannan an raunata wasu da-dama a lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai hari a garin Damasak, jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa sojojin Boko Haram tare da kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP su ka kai wannan hari a karamar hukumar Mobbar.
Rahotannin sun tabbatar da cewa an kai wadannan hare-haren ne a ranar Asabar, 10 ga watan Afrilu, 2021, wanda ya yi sanadiyyar raunata wasu sojojin kasa.
KU KARANTA: B/Haram: MNJTF sun yi galaba, 'yan ta’adda su ka barke da rikicin cikin gida
A cikin wadanda ‘yan ta’addan na Boko Haram su ka hallaka har da mata uku, da wani mutum daya, da wasu jami’ai uku daga cikin dakarun sojojin kasar.
Amma a wani kaulin, adadin wadanda ‘yan ta’addan na Boko Haram su ka kashe sun zarce hakan.
Majalisar dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da wannan hari da aka kai, ta ce dubban mutane za su iya gamu wa da matsala a sanadiyyar wannan danyen aiki.
A wannan hari, mayakan Boko Haram sun tarwatsa wani gini na majalisar dinkin Duniya inda duk wasu jami’an kungiyoyin kasashen waje su ke samun mafaka.
KU KARANTA: Jihohin Kudu m/gabas sun hada-kai, sun kafa Jami’an tsaro na musamman
‘Yan ta’addan sun dura garin Damasak ne da yamma, su ka shiga buda wa jami’an tsaro wuta ta ko wani bangare, a karshe su ka rusa wadannan gine-gine na UN.
A lokacin da wasu su ke kai wa sojoji hari, wasu ‘yan ta’addan sun maida hankali ne wajen kona dakunan ajiyan kungiyoyin kasashen waje da ke kusa da gine-ginen.
Har ila yau an taba gidan Sarkin Damasak, da ofishin hukumar Norwegian Refugees Commission a Fulatari, sannan aka saci kayan abinci a rumbun kungiyar WFP.
Shekarun baya aka kafa wannan gini a garin Damasak da ke kusa da rafin jihar Yobe domin bada gudumuwa ga wadanda hare-haren Boko Haram su ka shafa.
A karshen watan da ya wuce ne aka ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan wasu 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Chibok, a jihar Borno.
Asali: Legit.ng