Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato

Ke duniya ina zaki damu ne, yayin da ake zaton wuta a mekara sai gata an tsinceta a masaka, anan dubun wani Malamin makarantar allo ne ta cika bayan kamashi da laifin yi ma kananan yara almajirai fyade irin na luwadi, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dalibai da dama na makarantar allon dake unguwar Arkilla a cikin garin Sakkwato sun tabbatar da cewa malaminsu mai suna Murtala Muade ya sha yi musu fyade, haka zalika sun ce yana bayar da hayarsu ga yan luwadi suna amfani dasu.

KU KARANTA: Babu aiki ranar Laraba saboda za’a rantsar da Buhari karo na biyu – Gwamnati

Ke duniya! Kalli Malamin dake yin luwadi da almajiransa, kuma yana bada hayarsu a Sakkwato
Maude
Asali: Facebook

Malam Maude ya amince da wannan zargi, sai dai yace shi yasan yara uku kacal ya taba yi ma fyade, amma an samu wasu almajirai uku da suka bayyana kansu, inda suka ce suma yana musu fyade, wanda hakan ya kawo adadin daliban da malamin yake zakke mawa zuwa shida.

Kwamishinan Yansandan jahar Sakkwato, Ibrahim Kaoje ya bayyana cewa a ranar 22 ga watan Maris ne wani lauya dake aiki da hukumar kare hakkin biladama ta kasa, Hamza Liman ya kai karar malamin zuwa ofishin DPO na Yansandan Arkilla, daga nan aka mika maganar zuwa shelkwatar Yansanda.

Kwamishinan yace duka duka shekarun yaran bai haura 4 zuwa 15 ba, kuma yawancinsu yan Zamfara ne, amma Malamin ya mayar dasu abin huce sha’awarsa, har ma yana bayar dasu haya tamkar karuwai, don haka kwamishina Kaoje ya gargadi iyaye dasu daina kai yaransu almajiranci nesa da gida.

Amma abinka da ja’irin Malami, yayin da yake ganawa da manema labaru, sai ya kada baki yace kaddara ce, dama can Allah Ya kaddara sai yayi ma almajiran nasa fyade.

Zuwa yanzu dai an garkame wannan makarantar allo, kuma Yansanda sun kaddamar da bincike akan wannan lamari mai muni, sa’annan an mika almajirai shidan zuwa ga gidauniyar ceton yara, yayin da kungiyar lauyoyi Musulmai suka dauki nauyin ciyar dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel