Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da Aminin Buhari, Marigayi Mahmud Tukur
A ranar Juma’a, 9 ga watan Afrilu, 2021, Dr. Mahmud Tukur ya rasu bayan gajerar rashin lafiya a garin Abuja. Tun a ranar aka birne shi a Yola, jihar Adamawa.
Wannan karo, legit.ng Hausa ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin Marigayi Mahmud Tukur.
1. Haihuwa
An haifi Mahmud Tukur ne a shekarar 1939 a garin Yola, jihar Adamawa. Marigayin ya rasu kenan ya na da shekara 82 a Duniya.
Cikin ‘yanuwan Tukur na jini akwai Injiniya Hamman Tukur da ya yi aiki a Kad Poly, NEPA da RMFAC da kuma babban ‘dan siyasa Alhaji Bamanga Tukur.
2. Karatu
Bayan karatun firamare da sakandare a gida, Marigayin ya tafi wata jami’a a kasar Wales ya samu digirinsa a fannin ilmin siyasa da harkokin kasar waje.
Daga baya Tukur ya tafi jami’ar Pittsburg da ke kasar Amurka ya yi digirinsa na biyu a kan ilmin harkokin kasar waje.
KU KARANTA: Jami’o’in da za su shigo gari a Najeriya bayan samun lasisin NUC
Bayan nan ya dawo fitacciyar jami’ar nan ta gida, Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yi digiri na uku watau PhD.
3. Aiki
Marigayin ya yi aiki a jami’ar Ahmadu Bello har ya zama Darekta a tsangayar koyar da aikin gwamnati.
Daga nan ya tafi makarantar Abdullahi Bayero ta Kano a 1975, bayan ta zama jami’a, ya zama shugabanta na farko a 1977.
Tukur shi ne shugaban kamfanin Fukarabe Industries Ltd, kuma darekta a kamfanin Cadbury, sannan shi ya ke kula da Policy Analysis Ltd.
4. Shiga gwamnati
Tukur ya yi aiki a kwamitin da Adebo da Udoji su ka jagoranta wajen karin albashi a gwamnatin tarayya a 1976.
KU KARANTA: Tsohuwarmu ta yi wa Ni da Adda, Halima, Zahrah, Hanan komai - Yusuf Buhari
Bayan nan, Tukur ya na cikin wadanda su ka sa hannu wajen tsara kundin tsarin mulki na 1976 da 1996 da shirin Vision 2010 na 1997.
A 1984 ne aka nada Mahmud Tukur a matsayin Ministan sana’o’i da masana’anta, bayan ‘yan watanni a kan mulki ya bar kan karaga.
5. Rubuce-rubuce
Marigayin ya rubuta littafin “Leadership and governance in Nigeria : The Relevance of Values” a shekarar 1999.
Asali: Legit.ng