Okorocha: Fatara da rashin adalci ne tushen Boko Haram da EndSARS

Okorocha: Fatara da rashin adalci ne tushen Boko Haram da EndSARS

- Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana dalilan da suke janyo rashin tsaro a Najeriya

- A cewar Rochas, rashin adalci da fatara ne suka janyo zanga-zangar EndSARS, Boko Haram da sauransu

- Ya bayyana hakan ne a Ibadan a ranar Asabar yayin jawabi bayan kungiyar CCII sun karrama shi

Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo ya ce zanga-zangar EndSARS ta zalincin 'yan sanda, Boko Haram da sauran matsalolin tsaro suna aukuwa ne sakamakon fatara da rashin adalci.

Yayin da Rochas yake amsar jinjinar "Abokin mutanen Ibadan na musamman" da CCII suka gabatar masa a ranar Asabar ya bayyana hakan.

Jinjinar da Saliu Adetunji, Olubadan na Ibadan ya baiwa Rochas bisa kula da kokarinsa na tallafawa ilimin yaran talakawa da marayu a shirinsa na bayar da ilimi kyauta a makarantun Ibadan, jihar Oyo.

KU KARANTA: Ko ɗan da na haifa aka sace ba zan biya kudin fansa ba, zan yi addu'ar shigarsa aljanna, El-Rufai

Okorocha: Fatara da rashin adalci ne tushen Boko Haram da EndSARS
Okorocha: Fatara da rashin adalci ne tushen Boko Haram da EndSARS. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Yayin da yake jawabi, ya bayyana irin takaicin da yake tsintar kansa akan matsalar ilimin marayu da yaran talakawa a fadin Najeriya, The Cable ta wallafa.

A cewarsa, "Na samar da shirin ne ba don iyalina ba sai don kawar da rashin adalci da fatarar da take addabar kasarmu.

"Fatara da rashin adalci ne musabbabin Boko Haram, rashin tsaro, rikicin makiyaya da zanga-zangar EndSARS.

"Idan aka bar yaran nan babu ilimi mai inganci za su girma ne su zama 'yan ta'adda maimakon zama likitoci ko lauyoyi don taimakon al'umma.

"Na san saboda dan karamin kokarin da nake yi ne don taimakawa yaran nan marasa galihu ya janyo aka bani wannan jinjinar.

"Kuma wannan jinjinar zata kara janyo hadin kai tsakanin 'yan Najeriya saboda ni dan kabilar Ibo ne amma Yarabawa sun karramani."

A cewar CCII, fiye da yara 25,000, wandanda a kalla akwai 'yan jihar Oyo 6000 ne suka amfana daga tallafin Okorocha na ilimi ga marasa karfi.

KU KARANTA: Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu

A wani labari na daban, Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban sojin kasa, ya kamanta kungiyoyin IPOB da OPC da kungiyar Boko Haram.

A cewarsa OPC da IPOB suna yunkurin tayar da tarzomar kabilanci a Najeriya. Ya yi wannan bayanin ne a ranar Juma'a a Abuja, inda Dambazau ya bayyana kamanceceniyarsu da Boko Haram wacce ta fara a 2009.

Ya yi bayani akan yadda suke nuna zakewa da kuma kawo cikas.

"Ba jihohi suke yi wa yaki ba: suna da wata manufar ta daban ta raba kan al'ummar kasar Najeriya. Basu yarda da hadin kai ba kamar yadda Boko Haram take," a cewar Dambazau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng