Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu

Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu

- Mabiya Malam Abduljabbar Kabara sun yi kira ga Ganduje da ya bude musu masallaci don samun ladan Ramadan

- Dama an kulle masallacin ne tun bayan sabani ya auku tsakanin malamin da sauran malaman addinin musulunci

- Mai magana da yawun mabiya malamin ya musanta zargin da ake yi wa shugabansu inda ya kwatanta shi a matsayin mai son zaman lafiya

Mabiya Malamin nan na jihar Kano, Abduljabbar Kabara, sun yi kira ga Ganduje da yayi gaggawar bude musu masallaci don su mori ladan watan Ramadana.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, dama an rufe masallacin tun bayan malamin ya samu sabani da wasu malaman addinin musulunci.

Mai magana da yawun almajiran malamin, Iman Mohammed Rabiu Zakariya, ya musanta duk zargin da ake yi wa malamin, inda ya bayyana cewa shine malami mafi son zaman lafiya a Najeriya.

KU KARANTA: Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'

Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu
Gabatowar watan Ramadan: Mabiya Abduljabbar sun roki Ganduje ya bude masallacinsu. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF

"Mu almajiransa ne kuma mabiyansa, muna rokon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya taimaka ya bude mana masallaci don musulman jihar su amfana," a cewarsa.

Ya roki gwamnan da ya kara samar da damar mukabala tsakanin malaman addini a Kano don ya tabbata ba a fahimci malaminsu bane, domin Abduljabbar ba zai taba zubar da kimar ma'aikin Allah ba.

Batun cewa Abduljabbar mabiyin shi'a ne, Zakariya ya musanta hakan inda yace baya bin wata akida.

A cewarsa akwai 'yan Tijjaniyya, Shi'a, Kadiriyya da 'yan Izala da suke zuwa kwasar karatu wurin malamin.

Ya roki sauran malamai masu bambancin akida da Abduljabbar da su daina zubar masa da mutunci.

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.

Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.

Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel