Da duminsa: An tura 'yan sanda tsaron yankunan Hausawa a Imo

Da duminsa: An tura 'yan sanda tsaron yankunan Hausawa a Imo

- An tura jami'an 'yan sanda yankin Ama Auwsa dake birnin Owerri na jihar Imo domin baiwa Hausawa kariya

- Hakan ta faru ne domin dakile hare-haren da ake kaiwa Hausawa mazauna yankin kudu maso gabas a Najeriya

- Garkuwan Hausawa na yankin, yayi kira ga Hausawa dake arewa da kada su ce zasu yi ramuwar gayya

An tura jami'an tsaro yankin Ama Awusa, yankin da mafi yawan mazauna wurin 'yan arewa ne a garin Owerri, babban birnin jihar Imo.

An yi hakan ne sakamakon hare-haren da ake kaiwa 'yan arewa a yankin kudu masu gabas.

A makon da ya gabata, an kashe 'yan kasuwa bakwai 'yan asalin arewa a garin Orlu da Umuaka a karamar hukuma Njaba dake jihar Imo.

KU KARANTA: Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa

Da duminsa: An tura 'yan sanda tsaron yankunan Hausawa a Imo
Da duminsa: An tura 'yan sanda tsaron yankunan Hausawa a Imo
Asali: Original

KU KARANTA: Al'amuran 'yan bindiga ke kashewa da dakile cigaban arewa, ACF

A ranar Juma'a, babban mataimaki na musamman ga Gwamna Hope Uzodinma a kan jinsi, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, ya sanar da Daily Trust cewa an samar da isasshen tsaro don gujewa cigaban hare-hare.

Sulaiman, wanda aka fi sani da Garkuwan Hausawa, ya ce an wayar da kan jama'a a kan bukatar zama lafiya da makwabtansu.

Ya ce jama'a sun dauka kisan da aka yi a matsayin waani hukunci na Allah a maimakon tunanin daukan fansa.

"Mu bar wa Allah komai. Daga wurin shi muka zo, kuma can zamu koma. Wasu daga cikinmu sun dade a nan. Hatta kakanninmu sun kai shekara 150 a nan. A don haka muke ganin kanmu a matsayin 'yan jihar kuma babu amfanin fada da juna," yace.

Sulaiman ya shawarci 'yan arewa da ke barazanar kai hari ga Ibo a arewa da kada su shiga wannan siyasar da zasu yi nadama daga baya.

A wani labari na daban, Femi Adesina, kakakin shugaban kasa ya ce ba matsalar rashin tsaro kadai Najeriya take fama da ita ba, tana fuskantar "yakin harsuna".

A cewar Adesina, caccaka da kushe da wannan gwamnatin take fuskanta ya yi yawa. Wasu mutane sun sadaukar da rayuwarsu wurin runtse ido daga ganin wani amfani da kokarin wannan gwamnatin.

Ya bayyana wannan tunanin nasa a wata wallafa da ya fitar a Facebook ranar Alhamis, inda ya gabatar da matsalolin da Najeriya take fuskanta na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki kuma yaja kunnen masu kushe akan kada su yi amfani da damar da aka basu na tofa albarkacin bakunansu wurin zagin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel