Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar gwamnatin Buhari a wasu lokuta

Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar gwamnatin Buhari a wasu lokuta

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari tace kwadayi da kaunar mulki nagari yasa take caccakar mulkin mijinta

- Hakan yana kunshe a littafin tarihin Aisha Buhari da aka kaddamar a ranar Alhamis a fadar shugaban kasan

- Sanannen abu ne cewa uwargidan shugaban kasan ta saba kalubalantar mulkinsa tun hawansa karon farko

Aisha, matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana yadda take ji game da mulkin mijinta wanda take kalubalanta a wasu lokuta.

A littafin tarihinta da aka kaddamar a ranar Alhamis, uwargidan shugaban kasan tace tana caccakar gwamnatin ne saboda yadda take kaunar shugabanci nagari.

A littafinta, Aisha Buhari ta bayyana yadda aka aurar da ita a kananan shekaru da kuma martanin da tayi wa shugaban kasan a kan tsokacin da yayi na cewa madafi ne huruminta.

KU KARANTA: Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'

Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar Buhari a wasu lokuta
Aisha ta bayyana dalilinta na kalubalantar Buhari a wasu lokuta. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa

"A 1989, matashiyar ta aura Muhammadu Buuhari, soja mai mukamin Manjo janar da yayi ritaya kuma tsohon shugaban kasan Najeriya. Aisha kamar kowacce yarinya, ta sha gwagwarmaya da kalubale daban-daban na farkon aure," littafin yace.

"Ta aura mijin da kowacce mace za ta so alaka da shi, mai mutunci da daraja. Auren da tayi da wuri gareta ya zamo kalubale."

Tun bayan da Buhari ya hau shugabancin kasa a 2015, Aisha ta yi magana a kan rashin gamsuwa da wasu lamurran mulkin kusan sau uku.

Kasa da shekaru biyu da hawansa mulki, ta yi barazanar kin goyon bayansa ya zarce matukar abubuwa basu sauya ba a Najeriya.

A 2019, watanni bayan Buhari ya zarce, Aisha ta yi ikirarin cewa "mutanen banza" sun karbe gwamnatin kasar kuma mijinta na kallo

A cikin littafin, wanda Hajo Sani, hadimar shugaban kasa ta rubuta, ya ce duk da tana caccakar masu zagon kasa ga kudirin Buhari, babu alamar cin zarafi ko rashin ganin girmansa a caccakar da take yi.

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da 'yan Najeriya mazauna London suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin hari ne aka kaiwa arewa.

Tun a cikin watan Maris shugaban kasa ya bar Najeriya ya wuce London don a duba lafiyarsa.

Dama Buhari ya tsiri zuwa London tun da ya hau kujerar shugaban kasa a 2015, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel