Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN

Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta ce ta yarda Sojoji mata da jami'an tsaro mata su sanya Hijabi muddin zai karesu daga harsashin bindiga a filin daga.

Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Daramola, ya bayyana hakan a hirar da yayi da jaridar ThePunch ranar Alhamis.

Daramola ya yi tsokaci ne kan dokar da ake shirin kafawa a majalisar wakilai da zai hallatawa Sojoji mata sanya Hijabi.

Mataimakin shugaban kwamitin kudi na majalisar kuma mai wakiltar mazabun Bida/Gbako/Katcha, Saidu Abdullahi, ne ya gabatar da wannan kudiri.

Sashe na 13 na kudirin yace, "Dokar za ta haramta nuna bangaranci lokacin daukan aiki don mace ta sanya Hijabi."

KU DUBA: PDP: Ana musayar yawu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Aminu Tambuwal

Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN
Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

DUBA NAN: Miji na ya sake ni, ku taimakeni: Matar da ta zana hoton Tinubu a bayanta ta kai kuka Tuwita

Sakataren CAN ya cewa a kasashe irinsu Bida/Gbako/Katcha, matansu na sanya Hijabi saboda haka ba matsala bane da ya kamata ya dauke hankalin yan majalisa daga abubuwa masu muhimmanci irinsu tsaro da tattalin arziki.

Daramola yace, "Idan suka ga dama su sanya yar siket ko babbar riga. Idan Hijabin zai karesu daga harsashi, su sanya, tun da abinda suke so kenan."

Za ku tuna cewa Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta dakatad da wani shiri da ake yi a majalisar wakilai na yunkurin halasta amfani da Hijabi a makarantu a fadin tarayya.

A jawabin da Sakatare Janar na kungiyar CAN, Joseph Bade Daramola, ya sake, ya yi gargadin cewa wannan doka bai kamata a wannan lokaci ba, Punch ta ruwaito.

Kungiyar Kiristocin ta kara da cewa halasta sanya Hijabi zai tayar da tarzoma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel