'Yan Boko Haram sun sace mata 30 bayan kashe mutum biyar a Adamawa

'Yan Boko Haram sun sace mata 30 bayan kashe mutum biyar a Adamawa

- 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyen Kwapre da ke jihar Adamawa

- Sun halaka mutane guda biyar sannan sun yi awon gaba da mata a kalla guda 30 bayan lalata gidaje da dukiyoyi

- Hon Yusuf Buba Yakubu, dan majalisa mai wakiltar Gombi/Hong ya tabbatar da afkuwar harin da ya ce koma baya ne

Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Kwapre da ke karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa in suka halaka mutane biyar.

Sun kuma yi awon gaba da mata akalla 30 yayin harin da suka kai a ranar Juma'a da yamma a cewar The Nation.

'Yan Boko Haram sun sace mata 30, sun kashe 5 a ƙauyen Adamawa
'Yan Boko Haram sun sace mata 30, sun kashe 5 a ƙauyen Adamawa. Hoto: @channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi

Majiyoyi sun kara da cewa yan ta'addan sun rika harbe-harbe wadda hakan ya sa mutane suka tsere cikin daji kafin suka sace kaya tare da lalata gidaje.

Wani mazaunin garin, Geoffrey, wanda ke zaune kusa da garin da abin ya faru ya ce mutanen garin duk sun tafi wasu wuraren da suke ganin za su samu kariya.

"A halin yanzu babu ko mutum daya a Kwapre. Kowa ya bar garin," Innocent ya ce a wayar tarho a ranar Asabar.

Dan majalisa mai wakiltar mazabun Gombi/Hong a majalisar wakilan tarayya, Hon Yusuf Buba Yakubu ya tabbatar da harin da aka kaiwa garin.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa

Kwapre na kan iyakan jihar Adamawa da Borno ne kuma yana kusa da dajin Sambisa.

Kakakin yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje ya shaidawa ya ce Boko Haram ce ta kai harin don haka ba shi da hurumin magana a kai.

23 Armoured Brigade da ke Yola da garin ke karkashinta ita ma bata yi tsokaci ba.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164