Jiya ba yau ba: Tsoffin hotunan biloniyoyi Dangote, Adenuga da Otedola sun bada mamaki
- Femi Otedola, Mike Adenuga da Aliko Dangote sun kwashe tsawon shekaru suna abota ga kuma yalwatar arziki
- Otedola ya wallafa hotunansa da abokansa yayin da ake shagalin bikin cikar mahaifiyarsa shekaru 70 a 2002
- Take a nan ma'abota amfani da kafafen sada zumunta suka fara tsokaci iri-iri suna nuna wa abokan soyayya
Biloniyoyin 'yan kasuwar nan kuma abokan juna na tsawon shekaru, Femi Otedola, Mike Adenuga da Aliko Dangote sun bayyana wa duniya irin dadewar da suka yi cikin abota da kaunar juna har da wallafa tsofaffin hotunansu.
Otedola ya wallafa hotunansu tare a shafinsa na Instagram wanda suka dauka a ranar 3 ga watan Afirilun 2002 lokacin da mahaifiyarsa take bikin cikarta shekaru 70 a duniya.
A dayan hoton, an ga Otedola tare da mai kamfanin Globacom. Yayin da a dayan hoton an gan shi tare da Dangote yana shan ruwan gora.
KU KARANTA: 2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu
KU KARANTA: DSS tayi martani akan zarginta da ake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari
Kamar yadda ya wallafa: "Tuna baya, tun Juma'a 3 ga watan Afirilun 2002 (Shekaru 19 kenan) yayin da ake bikin cikar mahaifiyata shekaru 70. Shekaru sai kara lulawa suke yi don yanzu ta cika 89."
Take anan jama'a suka yi ta tsokaci suna yi musu fatan alkhairi.
Wata queenagnes_purelady cewa tayi: "Ubangiji yaja kwana kyakkyawar kakarmu."
Wani Hussaini_john_fashanu yayi tsokaci da: "Abin burgewa."
Officialjasonwilson yayi tsokaci da "Abin burgewa, muna wa mahaifiyarka fatan alkhairu."
Toyin.Olagoke351 yace: "Tarihi mai bada sha'awa."
A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.
Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.
Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.
Asali: Legit.ng