Bashir El-Rufai: A kan me 'yan arewa zasu bukaci lasisin tuki a kasar da take mallakinsu

Bashir El-Rufai: A kan me 'yan arewa zasu bukaci lasisin tuki a kasar da take mallakinsu

- Dan gwamnan jihar Kaduna ya yi tambaya akan dalilin da zai sa ace a kasar nan har sai dan arewa ya bukaci lasisi kafin yayi tuki

- Bashir El-Rufai ya yi wannan tambayar ne a matsayin amsa ga wani mutum wanda yayi wata wallafa a shafinsa na Twitter

- A cewar mutumin, dan arewa zai iya shekaru 20 yana tuka motarsa ba tare da ya mallaki shaidar kwarewa a tuki ba

Dan gwamnan jihar ya yi tambaya akan idan wajibi ne dan arewa ya mallaki shaidar samun izinin tuki akan abin hawarsa a kasar da mallakinsa ce.

Bashir El-Rufai ya mayar wa da wani martani ne a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, yayin da mutumin yace a arewacin Najeriya mutum yana iya shekaru 20 yana tuki ba tare da yana da shaidar kwarewa a tuki ba.

Kamar yadda mutumin ya wallafa, "Kana iya kwashe shekaru 20 ba tare da shaidar kwarewa a tuki ba a arewa".

A nan ne dan gwamnan ya mayar da martani, inda yace "Menene dalilin da zai sanya sai dan arewa ya nemi lasisin tuki a motarsa da titunan cikin kasar da ta zama tashi?"

KU KARANTA: 2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu

Bashir El-Rufai: A kan me 'yan arewa zasu bukaci lasisin tuki a kasar da take mallakinsu
Bashir El-Rufai: A kan me 'yan arewa zasu bukaci lasisin tuki a kasar da take mallakinsu. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Wannan tambayar tasa ta janyo cece kuce a shafinsa na Twitter, wanda 'yan Najeriya suka yi ta tofa albarkacin bakunansu.

KU KARANTA: Tinubu ya sake kwapsawa bayan ya kira Dolapo Osinbajo da 'matar shugaban kasa'

Wani mai amfani da suna @itopa7 cewa yayi, "A tunanina ya zama dole, ta yadda za a samar da nau'in natsuwa a tsakanin direbobi. Wasu na amfani da dama ba yadda ya dace ba."

@kaycdgreat cewa yayi, "Duba abinda dan gwamna ke cewa, mutumin da ya dace ya zama misali nagari ga wasu yana cewa baya bukatar lasisin tuki a 2021. A karni na 21."

@shekNettan cewa yayi, "A gaskiya Bash bai yi daidai ba, ku kira shi da gatse ko komai. Amma za a yi amfani da martaninsa na gaba kadan a kan shi. Amma ina son in gane wacce daga cikin arewan yake magana. In kuma arewacin Najeriya ce toh."

A wani labari na daban, a wata takarda ta ranar Alhamis wacce Matawalle ya tura ya bayyana zanga-zangar a matsayin al'amari da wasu suka dauki nauyi, kuma wadanda suka shirya basu da wayewa.

Ya kuma ja kunne akan kaiwa 'yan arewa hari da kuma sana'arsu a kudu.

"Na yi Allah wadai ta yadda kullum ake nuna tsana ga dan arewa kuma hakan ya zarce har suka kaiwa Buhari hari saboda masu zanga-zangar ba zasu iya boye tsana da hassadar da suke yi wa 'yan arewa ba. "

Source: Legit Nigeria

Online view pixel