Manyan Jami'an Sojin Ƙasar nan sun gana kan yawaitar Hare-Haren da ake kai ma hukumomin tsaro

Manyan Jami'an Sojin Ƙasar nan sun gana kan yawaitar Hare-Haren da ake kai ma hukumomin tsaro

- Manya-Manyan jami'an sojojin ƙasar nan sun gana kan yawaitar kai hare-hare da ake kaima hukumomin tsaro musamman a yankin kudu maso gabas

- Jami'an sojin sun fara tattauna yadda zasu ƙara tsaurara tsaro a wuraren da jami'ansu suke dan gudun abubuwan dake faruwa su dawo kansu

- Sun ce zasu tattauna da duk masu ruwa da tsaki a dukkan yankunan ƙasar nan shida, don su gargaɗi matasa kada su shiga irin waɗannan matsalolin

Manyan jami'ai daga hedkwatar tsaro ta ƙasar nan tare da masu faɗa aji daga hukumomin tsaro na sojoji sun yi wata ganawar sirri a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Muggan makamai Sama da miliyan 6 ke shawagi a faɗin ƙasar nan, Inji Janar Abdussalami

Jami'an tsaron soji sun gana ɗin ne kan yawaitar hare-haren da ake kaiwa jami'an tsaro musamman a yankin kudu masu gabashin ƙasar nan.

Taron an yi shi ne a Otal ɗin Transcorp dake babban birnin tarayya, Abuja kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyana cewa jami'an tsaron sojojin sun tattauna kan yadda za'a daƙile kai harin wanda ake zargin mambobin ƙungiyar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) ke yi.

Manyan Jami'an Sojin Ƙasar nan sun gana kan yawaitar Hare-Haren da ake kai ma hukumomin tsaro
Manyan Jami'an Sojin Ƙasar nan sun gana kan yawaitar Hare-Haren da ake kai ma hukumomin tsaro Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Majiyar ta cigaba da cewa, jami'an sun nuna matuƙar damuwa kan cewa maharan ka iya dawo kan jami'an sojojin da zarar sun gama da yan sanda a yankin.

KARANTA ANAN: Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri

A cewar majiyar:

"Jami'an sojin sun ɗauki lamarin da muhimmanci, domin har sun fara shirye-shiryen ganin ba'a kai hari ga wuraren da jami'an soji suke ba, kamar yadda aka kai hari ga hedkwatar hukumar yan sanda da kuma jami'an tsaron dake kula da gidan gyaran hali a jihar Imo."

Sun kuma tattauna kan zama da masu ruwa da tsaki daga dukkanin yankunan ƙasar nan guda shida da muke dasu, da nufin gargaɗin matasa kada su kuskura su shiga cikin masu aikata wannan aiki daga kowanne yanki.

A lokacin da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Brig.-Gen. Mohammed Yerima, ya bayyana cewa an gayyace su Otal ɗin ne kan wani taro kawai.

A wani labarin kuma Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000.

Shugaban kwamitin yaƙi da cutar korona, Boss Mustapha ne ya bayyana haka a taron da kwamitinsa ya saba yi duk sati

Mustapha ya ce suna fatan yiwa 70% na yan Najeriya allurar rigakafin a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel