Sojin Najeriya sun mamaye garinsu ministan Buhari, suna zuba ruwan wuta

Sojin Najeriya sun mamaye garinsu ministan Buhari, suna zuba ruwan wuta

- Yanzu haka sojojin Najeriya sun mamaye karamar hukumar Essien Udim dake jihar Akwa Ibom

- Hakan ya biyo bayan yadda wasu 'yan bindiga suka ragargaji jami'an tsaron yankin har suka kashe wasu

- Tuni mazauna yankin suka tsere zuwa wasu wuraren na daban bayan sojojin sun umarcesu da hakan don samun tsira

Yanzu haka sojojin Najeriya sun fara ayyukansu na binciko wasu 'yan ta'adda da suka kai hari karamar hukumar Essien Udim dake jihar Akwa Ibom.

Ministan harkokin Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio dan karamar hukumar ne wacce jami'an tsaronta suka fuskanci wannan harin.

Dama a makonnin da suka gabata, 'yan bindigan da ba a san ko su waye ba sun kai hari a jihohin kudu maso gabas da kudu-kudu.

Har yanzu dai minista Akpabio bai riga ya ce komai ba akan ayyukan da sojoji suke yi.

KU KARANTA: Gwamnonin APC sun gwangwaje 'yan kasuwar da gobara ta shafa da N50m a Zamfara

Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji garinsu ministan Buhari
Dakarun sojin Najeriya sun ragargaji garinsu ministan Buhari. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun shirya yin sasanci da ƴan bindigan da suka sace ƴaƴanmu, Iyayen ɗaliɓan Kaduna

The Nation ta ruwaito yadda sojoji suka fara ragargazar duk wasu wurare da ake zargin maboyar 'yan ta'adda ne a ranar Talata, 6 ga watan Afirilu.

Kamar yadda rahoton yazo, an turo jirage da dama don tabbatar da tsaro a yankin.

A ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu sojojin yankin suka umarci mazauna wurin da su yi gaggawar barin yankin don gudun kada wasu marasa gaskiya su boye a gidajensu.

Sai da aka kori dalibai daga jami'an Federal Polytechnic Ukana dake karamar hukumar Essien Udim wacce bata da nisa da gidan Akpabio don a samu a rufe makarantar.

A kalaman jami'in hulda da jama'a na sojin ya ce "Yanzu haka bamu san ko su waye ba, menene niyyarsu sannan kuma wanene ya turosu ba."

A makon daya gabata, sai da suka kashe 'yan sanda 3, ciki harda wani CSP na 'yan sanda bayan an kai musu hari har yanzu ba a san inda wasu 4 suke ba.

A wani labari na daban, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumuntar zamani wanda aka ga wasu matasan jihar Kogi dauke da bulalai suna tsabga wa wasu matasa biyu da suke zanga-zangar nuna kiyayya ga Shugaba Muhammadu Buhari.

A bidiyon wanda Premium times ta wallafa a ranar Litinin, 5 ga watan Afirilu an ga matasan suna cire 'Buhari Must Go' daga jikin bango ana basgarsu da bulalai a mazaunansu.

Sun umarci matasan da su sake yin fenti a bango yayin da suke shan ruwan bulalai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel